Wani direba a Kogi ya hallakar da matarsa kan naira 2,000 kacal

Wani direba a Kogi ya hallakar da matarsa kan naira 2,000 kacal

- Wani direban motar haya a Kogi ya soka wa matarsa wuka har lahira

- Gaddama ta kaure ne tsakanin ma’auratan kan kudin abinci 4,000

- Mutumin ya ya nema a yi masa gafara cewa kuskure ne

Wani direban motar haya mai shekaru 30 daga Ihima a karamar hukumar Okehi da ke jihar Kogi, wanda aka sani da Garuba ya ce ya kashe matarsa, Falilat a kan kudin cafane 2, 000.

Ma’auratan sun yi aure tun shekaru 15.

Garuba ya ce: "Matana ta nema in bata kudi 4,000 domin ta saya kayan abinci. Amma 2,000 kawai nake da karfin bata a wannan lokacin, inda na mata alkawarin cewa san cikita mata washe gari.”

"Duk da haka, zai ta fara zagi na a lokacin da nace ta dawo da 500 cikin kudin, wanda nace zan yi amfani da shi don zirga-zirgar neman ma ta kari."

"Kafin na san abin da ke faruwa, ta kai mini mari, abin da ya bani fushi. Ni kuma na tsince wuka na soka ma ta a makogwaro."

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Garuba ya yi nadama aikata danyen aikin inda ya nema a yi masa gafara kuma ya nuna damuwarsa a kan yanayin kiwon lafiya dan su mai shekaru 15 da haihuwa.

KU KARANTA: Jami’an yan sanda sun damke mutum da sassan jikin mutum

mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da ayyuka, Yahaya Abubakar wanda ya wakilci kwamishinan' yan sanda jihar Kogi ya gabatar da Garuba tare da wasu 15 wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban a Jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Wannan tsohowar matan ta yi hasarar danta ga kungiyoyin asiri

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel