Munyi kuskure game da furucin da mukayi kan yan kabilar Igbo – Gamayyar matasan Arewa

Munyi kuskure game da furucin da mukayi kan yan kabilar Igbo – Gamayyar matasan Arewa

- Shugabannin kungiyar matasan arewa sunyi amai sun lashe bayan kuran da suka tayar

- Shugabannin sunce zasu bada daman tattauna soke-soken da akayi bisa ga furucinsu

- Game da cewarsu, Najeriya zata cigaba tamkar tsintsiya madaurinki daya

Gamayyar kungiyoyin matasan arewa ta janye maganar da tayi na baiwa yan kabilar Igbo wa’adin kwanaki 120 domin barin arewacin Najeriya kuma da cewa dukkan yan arewan da ke garuruwansu su dawo gida.

Da yammacin jiya, shugabannin kungiyar sun shiga ganawar gaggawa domin tattaunawa bayan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufai ya bayar umurnin damke wadanda sukay wannan furuci.

Munyi kuskure game da furucin da mukayi kan yan kabilar Igbo mazauna Arewa – Gamayyar matasan Arewa tayi amai ta lashe

Munyi kuskure game da furucin da mukayi kan yan kabilar Igbo mazauna Arewa – Gamayyar matasan Arewa tayi amai ta lashe

Daga baya, kakakin gamayyar Abdulaziz Suleiman yayi bayani wa manema labarai cewa : “Ya bayyana cewa matakin da muka dauka farko ba daidai bane. Akwai bukatan aiki tare a matsayin kasa daya.

KU KARANTA: Harin Boko Haram ya kori mutane daga muhallinsu

Wannan ba lokacin tattauna rabuwa bane. Akwai bukatan hada kai. Ba’a san arewa da rashin lumana ba.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel