Saudiya ta baiwa Najeriya kyautan kilo 181,437 na dabino

Saudiya ta baiwa Najeriya kyautan kilo 181,437 na dabino

- Gwamnatin kasar Saudiya ta aiko ma Najeriya kyautan dabino

- Jakada Dakta Yahaya Ali Mughram ne ya mika dabinon ga Najeriya

Gwamnatin kasar Saudiya ta aiko ma Najeriya kyautan dabino don a raba ma musulman Najeriya domin shan ruwa a watan Azumin Ramadana, inji rahoton Daily Trust.

Wata sanarwa daga ofishin jakadancin kasar Saudiya dake Abuja ta bayyana cewar shugaban ofishin jakadancin, Dakta Yahaya Ali Mughram ne ya mika dabinon ga karamar ministan harkokin wajen kasar nan, Hajiya Khadija Bukar Abba Ibrahim.

KU KARANTA: Matsafa na farautan masu sanƙo wurjanjan a kasar Mozambique

Mughram yace kasar Saudiya tayi wannan kyautan ne ga Najeriya don inganta dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu, sa’annan yayi fatan samun cigaba da zaman lafiya a kasashen biyu, kamar yadda majiyar NAIJ.com.

Saudiya ta baiwa Najeriya kyautan kilo 181,437 na dabino

Jakadan Saudiya yana mika minista kyautan

Da take bayani, minista Khadija Bukar ta bayyana godiyar gwamnatin Najeriya ga gwamnatin Saudiya, inda tace dantaka tsakanin kasashen biyu zata cigaba da karko.

Minista Khadija tace yan gudun hijira dake sansanin yan gudun hijira ne zasu fi cin moriyar wannan kyauta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yaya idan matarka tafi ka albashi?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel