Shanun makiyaya sun afka azuzuwan makarantar Firamari (Hotuna)

Shanun makiyaya sun afka azuzuwan makarantar Firamari (Hotuna)

- Shanun yan Fulani makiyaya sun mamaye makarantar Firamari

- Hakan yayi sanadiyyar korar dalibai da malamansu daga makarantar.

Wasu shanun yan Fulani makiyaya sun mamaye wata makarantar Firamari dake jihar Edo, wanda hakan yayi sanadiyyar korar dalibai da malamansu daga makarantar.

Jaridar Punch ta ruwaito wannan rahoton yadda Fulani ke yi ma dabbobinsu rikon sakainar kashi yayin kiwo, su kuma dabbobin su je su yi ta ma jama’a barna.

KU KARANTA: Anyi Artabu tsakanin jami’an Soji da mayaƙan Boko Haram a Maiduguri

Shuwagabannin makarantar Firamari ta Ohovbe dake garin Ikpoba, na karamar hukumar Okha na jhar Edo sun koka kan yadda makiyaya suka saki dabbobinsu sakaka, suka afka makarantar, suka mamaye azuzuwansu.

Shanun makiyaya sun afka azuzuwan makarantar Firamari (Hotuna)

Shanun makiyaya

Sakamakon hakan yasa malaman makarantar kwashe daliban daga azuzuwan, don gudun kada su illata daliban, ko su raunata su, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Shanun makiyaya sun afka azuzuwan makarantar Firamari (Hotuna)

Shanun makiyaya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Makafi 4 yan gida daya:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel