Gwamnan Bauchi ya biyawa daliban jihar kudaden WAEC, NABTEB, NECO da NBAIS

Gwamnan Bauchi ya biyawa daliban jihar kudaden WAEC, NABTEB, NECO da NBAIS

- Gwamnan jihar Bauchi ya biya wa daliban jihar kudaden jarrabawa na bana 2017

- Kwamishinan ilimi ya ce ilimantar da manyan gobe na cikin burin gwamnan jihar

- Gidado ya kuma ce jihar ta samu ci gaba daga kashi 3.65% (2015) zuwa kashi 17.6% (2017) a duka darussa

Gwamnan jihar Bauchi, M. A. Abubakar ya amince da fitar da naira miliyan 425 domin biya wa daliban jihar Bauchi kudaden jarrabawar WAEC, NABTEB, NECO da NBAIS na shekarar 2017.

Mataimakin gwamnan kuma kwamishinan ilimi, Nuhu Gidado shine ya bayyana haka a wata sanarwa da hadimin gwamnan a fannin sadarwa, Shamsuddeen Lukman ya fitar.

Gidado ya ce ilimantar da manyan gobe na daga cikin burace buracen mai girma gwamnan jihar. Yana mai cewa gwamnan na burin daga darajar jihar Bauchi a fagen ilimi.

Gwamnan Bauchi ya biyawa daliban jihar kudaden WAEC, NABTEB, NECO da NBAIS

Gwamnan jihar Bauchi, M. A. Abubakar da ministan kudi Kemi Adeosun

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, kwamishinan ya ce kuma kawo yanzu ana ganin alfanun hobbasar gwaman musamman idan akayi la'akari da cigaban da aka samu daga 2016 inda a jarrabawar WAEC aka samu cigaba daga kashi 3.65% (2015) zuwa kashi 17.6% a duka darussa ciki har da darasin lissafi da turanci. Yana mai cewa suna sa ran a samu kari a wannan shekarar.

KU KARANTA: 'Arewa na wasa da wuta' inji Femi Fani-Kayode

Mataimakin gwamnan ya kuma shawarci daliban da su dage da karatunsu domin baiwa marar da kunya. Yana mai cewa kokarin kowa zai kwaceshi ganin cewa yanzu babu cibiyar cuwa-cuwa da ake cin jarabawa a sama.

Mataimakin gwamnan ya kuma yabawa daliban jihar bisa yadda aka samu karancin satar amsar jarrabawa a 2015 inda bincike ya nuna satar amsa ta ragu da kashi 2% a jihar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga bidiyon inda mai martaba sarki Sanusi ya shawarci shugabannin Najeriya da shugabanci na nagari

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel