Mutane 8 sun hallaka, 37 sun jikkata a harin Boko Haram na Jiddari Polo

Mutane 8 sun hallaka, 37 sun jikkata a harin Boko Haram na Jiddari Polo

An samu wata tashin hankali jiya yayinda ake shan ruwa a Jiddari Polo, Maiduguri jihar Borno lokacin da yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram sukayi artabu da jami’an tsaro wnda aka kwashe sa’o’I ana musayan wuta.

Mazauna unguwan da suka arce jiya dare sun dawo da safen nan kuma sun tarar da cewa an kwashe dukiyoyinsu kuma an kona musu gidaje.

Mr. Philip Umoru wanda yayi magana da manema labarai ya mika godiya ga Allah da yak are iyalinsa, duk da cewa yayi asaran muhallinsa inda suka kona gidansa kurmus.

Mutane 8 sun hallaka, 37 sun jikkata a harin Boko Haram na Jiddari Polo

Mutane 8 sun hallaka, 37 sun jikkata a harin Boko Haram na Jiddari Polo

Laifyanmu kalau, amma ba dadi. Bamu san dalilin da yasa aka kawo harin ba bayan mun far tunanin komai ya lafa,”.

Wasu mazauna yankin sunce tashe-tashen Bam a kuma harbe-harben harsasai ya hallaka mutane 8 kuma jikkata 37 kuma suna asibitin jami’ar Maiduguri yanzu.

KU KARANTA: Dalilin da yasa rashawa tayi yawa a Najeriya- Kemi Adeosun

Wata majiya tace: “Wannan abun takaici ne. Nayi magana da wani idon shaidah a CBDA wanda yace sun kai gawawwaki 8 da wadanda suka jikkata 37 asibiti. Yace harin ya faru ne a wurare 4 dagan-daban, A kwaleji tekun Chadi, gaban kwalejin aikin noma, wata masallaci a Goni Kachallari.”

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel