Kuma dai, EFCC ta gano biliyoyin kadarori mallakar matar tsohon shugaban kasa

Kuma dai, EFCC ta gano biliyoyin kadarori mallakar matar tsohon shugaban kasa

- An binciki Uwargidan tsohon shugaban kasa Patience Jonathan kan wasu kadarori na biliyoyin naira da hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta gano

- Har ila yau ana bincikar matar tsohon shugaban kasar bisa alakar ta ga wasu kadarori guda uku

- Hukumar ta ce tana ci gaba da gudanar da binciken wadannan kadarori da dukiyoyi har sai sun kammala bincikensu

Hukumar yaki da cin hanci da hana yiwa tattalin arziki zagon kasa wato EFCC ta kara gano wasu tarin kadarori dake mallakar Patience Jonathan , uwargidan tsohon shugaban kasar Najeriya .

EFCC ta kaddamar da cewa dukiyoyin na karkashin bincike a yanzu sannan kuma ta ce ana iya sanya dukiyoyin a karkashin ikonsu.

KU KARANTA KUMA: Muna nan a kan bakarmu na kowani dan Kabilar Igbo ya koma ‘yankinsa – Kungiyar matasan Arewa

Rahoton ya bayyana cewa hukumar EFCC ta gano alakar dake tsakanin Mrs Patience Jonathan da wasu manyan Kamfuna bayan da injimin gano ilolin cin hanci suka gudanar da wata bincike akan wannan lamari.

Haka zalika, akwai wasu manyan Akawun uku dake cike da makudan kudade da wasu manyan kadarori uku da hukumar ke zargin suna da kyakyawan alaka da Mrs Patience Jonathan.

Hukumar dai har izuwa yanzu, tace tana cigaba da gudanar da binciken wadannan kadarori da dukiyoyi har sai sun kammala bincikensu

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon gangamin hukumar EFCC kan yaki da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel