Mujahid Asari Dokubo ya bayyana yadda yake so masu son Bayafara suyi da Najeriya

Mujahid Asari Dokubo ya bayyana yadda yake so masu son Bayafara suyi da Najeriya

- 'Mu da duk kabilun mu yan Biafra ne'

- 'Bamu ci arzikin kowa ba, bamu karbi kasar kowa ba, sai ma namu ake ci a arewa'

- Asari Dokubo yayi tsit tun bayan hawan shugaba Buhari, sai yanzu ya sami bakin magana

A musaya da martanin kalamai da ake tayi a satin nan kan batun da wasu shashashu daga arewacin Najeriya suka yi kan wai sun baiwa kabilar Ibo watanni ukku su fice su bar arewa, dan rajin kwace arzikin man yankin Neja Delta daga Najeriya Alhaji Mujahid Asari Dokubo, ya fito yayi zafafan kalamai kan batun.

A cewar Asari Dokubon dai ba wai kasar arewa ko arzikinta suke so ba, a'a, su so suke ma arewar ta rabu dasu ta dena ci musu arziki.

Yayi kira kuma ga kabilun yankin nasu dake zaune a kudancin kasar da kada su sake su bari ayi musu aika-aika kan lafiyarsu ko dukiyar su, da lallai su tashi su kare kansu in bukatar hakan ta taso.

Mujahid Asari Dokubo ya bayya yadda yake so masu son Bayafara suyi da Najeriya

Mujahid Asari Dokubo ya bayya yadda yake so masu son Bayafara suyi da Najeriya

"Muna da 'yancin kare kai, domin muna da 'yanci, zamu kare dukiyar mu da lafiyar mu, kuma dama mun yi duk yadda zamu yi don 'yanci a baya'.

"Sune ma suke cin arzikin mu, sun kankane kasar mu ta Bayafara, muna kira da su bar mana arzikinmu, su dena dogaro damu, mu bamu je musu kasa ba' ya kara da cewa.

"Kabilunmu shidda duk 'yan kasar Biyafara ne, kuma tsintsiya muke, da Ibon mu, Ibibio dinmu, Efik, Oron da Ogoni duk kanmu hade yake, kuma baza mu kwanta mu jira ba in aka zo kashe mu." cewar sa.

An dai sha jin Asari Dokubo na irin wadannan kalamai lokacin Goodluck Jonathan, amma tunda ya fadi zabe, aka dena jin duriyar da taratsin, ko tsoron Buhari yaji, oho?

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel