Korar Inyamurai daga Arewa: Da ma can wannan shirin Buhari da Jam’iyyar APC ne ga Kabilar Igbo – Kungiyar MASSOB

Korar Inyamurai daga Arewa: Da ma can wannan shirin Buhari da Jam’iyyar APC ne ga Kabilar Igbo – Kungiyar MASSOB

- Kungiyar MASSOB ta yi kira ga Inyamurai mazauna Arewa da su dawo gida

- Ta ce su zo su yi kokari don kafa kasarsu na Biyafara

- Kungiyar ta zargi shugaba Buhari da jam'iyyar APC da son muzguna masu

Kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biyafara, MASSOB ta yi kira ga ‘yan Kabilar Igbo da ke zaune a Arewacin kasar da su fara hada yanasu-yanasu su dawo gida.

Shugaban kungiyar Uche Madu ya ce kowani Inyamuri ya tattara komatsan sa ya dawo su gina yankinsu na Biyafara.

Ya ce dama wannan shiri ne da shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da jam’iyyarsa ta APC suka yi domin su muzguna wa kabilar Igbo a kasar.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya tofa albarkacin bakinsa kan barazanar da akayiwa Igbo

Duk da cewa Mallam Nasir El-Rufai ya umurci jami’an tsaro da su kamo shugabannin wadannan kungiyoyi sannan ma’aikatar shari’ar jihar ta shigar da kara akan hakan, MASSOB ta ce duk da hadin bakin shugabannin yankin Arewacin kasar.

Sakataren kungiyar Ohaneze Uche Achi-Okpaga ya roki ‘yan Kabilar Igbo din da su zauna da kowa lafiya sai dai kuma idan suka ga cewa ana yi wa rayuwarsu barazana to mutum ya dawo gida.

MASSOB ta ce babu abin da zai dakatar dasu daga neman kasarsu ta Biyafara kuma hakan ya sa cikin ‘yan Arewa ya duri ruwa ne bayan ganin yadda suka yi zaman kwanaki uku na nuna juyayi shekaru 50 da kafa Biafra.

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel