'Arewa na wasa da wuta' inji Femi Fani-Kayode

'Arewa na wasa da wuta' inji Femi Fani-Kayode

- Fani-Kayode ya ce wannan karon arewa zata sha mamaki in ta tada yaki

- Zamu tuna mata ba ita ce da kasar Najeriya ba a yanzu

- Ya ce hari a kan 'yan kabilar Ibo zai ruguza kasar nan

Zafafan kalamai daga dan zafi Fani-Kayode kenan a yayin da yake mayar da martani ga wasu 'yan taratsi a arewa suka yi barazana kan kabilar Ibo mazauna arewa, wanda tuni hukumo ma sun bada sammacin a kame su.

Dama dai an sha jin Fani Kayode na aman wuta kan batun bangaranci, siyasa, addini da ma kabilanci, inda yake zargin arewa da son mulkin mallaka da sauran kabilun kasar nan.

Ko a satin da ya gabata ma dai FFK ya yi ,kira ga kiristocin Najeriya da su tashi suyi jihadi da sunan Yesu a Najeriya, su ruguje masallatai da wuraren ibada na wasu, amma ba wanda ma ya amsa masa.

'Arewa na wata da wuta' inji Femi Fani-Kayode

'Arewa na wata da wuta' inji Femi Fani-Kayode

"Suna son su jefa Najeriya cikin wani duhu, amma zamu shiga duhun tare dasu, domin muma a shirye muke' inji shi.

"Masu son korar Ibo daga arewa su sani sun budo kofar jahannama ne, kuma zamu aika su cikinta, domin kabilar Ibo ba ita kadai bace, zamu shigar mata mu sauran mutanen kudu' Ya kara da cewa.

"Ina kira ga dattijan arewa dasu maza-maza su gyaro kan lamarin, in ba haka ba, ba wai yakin basasa kawai za'ayi ba, a'a, karshen Najeriya ne yazo", cewar sa.

An dai san Fani Kayode da zafi, tun lokacin fitarsa daga jam'iyyar APC, inda ya zarge ta da addinanci da kabilanci.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel