Anyi Artabu tsakanin jami’an Soji da mayaƙan Boko Haram a Maiduguri

Anyi Artabu tsakanin jami’an Soji da mayaƙan Boko Haram a Maiduguri

- Harin Boko Haram a garin Maiduguri ya sa jama’a barin gidajensu

- Da yammacin ranar Laraba 7 ga watan Yuni ne mayakan Boko Haram suka kai hari cikin garin Maiduguri

Da yammacin ranar Laraba 7 ga watan Yuni ne mayakan Boko Haram suka kai hari cikin garin Maiduguri da nufin mamaye unguwar Jiddari dake cikin garin, sai dai sun gamu da tirjiya daga rundunar sojin Nijeriya.

Harin dai ya faru ne a yankin Jiddari Polo, wata unguwa da ke wajen Maiduguri, a daidai lokacin da mutane ke shirin shan ruwa bayan azumin Ramadan.

KU KARANTA: Arzikin man fetur ɗin Najeriya, na Arewa ne – Inji Usman Bugaje

Rundunar Soji ta bada sanarwar dakatarwa tare da wargaza manufar mayakan Boko Haram din, kamar yadda NAIJ.com ta samu rahoto, an hallaka yan Boko Haram da dama, tare da jikkata wasu da dama.

Anyi Artabu tsakanin jami’an Soji da mayaƙan Boko Haram a Maiduguri

Mayaƙan Boko Haram

Daraktan watsa labaru na rundunar, Birgediya Kukasheka ya tabbatar da kai harin, inda yace sun mayar da biki akan yan Boko Haram, sa’annan sun kashe da dama daga cikinsu.

Musayar wuta tsakanin Sojoji da Boko Haram ya tilasta ma mazauna unguwar jiddari boyewa a cikin gidajensu, kamar yadda wata shaidar gani da ido, Janet Ibrahim ta bayyana, tace:

“Munji karar bindigu da alburusai sosai, ban san ko mutane nawa aka kashe ba, amma dai na san sunyi kokarin shigowa gari, amma Sojoji sun hana su.”

Jim kadan bayan hareharen sai jama’an yankin suka fara tserewa daga gidajensu zuwa sauran yankunan jihar, Janet ta cigaba da fadin “Yan Boko Haram sun tsere bayan da suka hangi jirgin sojojin sama”

Shima wani mazaunin yankin, Abraham Haruna, ya bayyana cewar “Dole tasa na tsere daga gidana, coci zan je in kwana.”

Irirn wannan hari, shine irinsa na farko, da Boko Haram suka kai tun bayan da Sojoji suka karya lagon su, sai dai wannan hari yazo ne a daidai lokacin da ake sa ran muƙaddashin shugaban Nijeriya, farfesa Yemi Osinbajo zai kai ziyarar aiki birnin Maiduguri ranar Alhamis.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Makafi yan gida daya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel