Wani abu sai a Najeriya: An ba dan tsohon minista izinin tafiya aikin umura bayan almundahana da biliyan 1.2

Wani abu sai a Najeriya: An ba dan tsohon minista izinin tafiya aikin umura bayan almundahana da biliyan 1.2

- Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Abuja taba dan tsohon minista izinin tafiya aikin umura bayan zargin sa da almundahana da biliyan 1.2

- Kotu ta amince da bukatar lauyan Bala na saki fasfonsa don ya samu ya yi aikin umura

- Alkalin kotun ya dage al’amarin har zuwa watan Yuni 26 domin ci gaba da shari’ar

Babbar kotun tarayya a Abuja a ranar Laraba, 7 ga watan Yuni ya ba Shamsudeen Bala, dan tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja izinin tafiya aikin Hajji.

Yawanci irin wannan iznin dai marasa lafiya a ke bawa masu bukatar jinyan gaggawa a kasar waje.

A lokacin ci gaba da sauraran karar a ranar Laraba,lauya mai bawa Bala shawara, Kanayo Okafor ya bukaci kotun da ta saki fasfo na kasa da kasa na Bala don ya samu ya yi aikin umura.

Wani abu sai a Najeriya: An ba dan tsohon minista izinin tafiya aikin umura bayan almundahana da biliyan 1.2

Shamsudeen Bala, dan tsohon ministan babban birnin tarayya Abuja wanda kotu ya ba izinin tafiya aikin umura

Amma Ben Ikani, lauya mai bawa hukumar EFCC shawara ya yi amayya da matakin, yana mai cewa lauyan mai kare Bala yana koƙarin jinkirta shari’ar ne kawai.

Bayan sauraron lauyoyin biyu, alkalin kotun Nnamdi Dimgba, ya ba Bala izinin tafiya aikin umura.

Alkalin ya bukaci cewa dole ne zai wani dan majalisa ya sa hannu a takada wanda zai tabbatar da cewa Bala zai dawo kasar bayan kammala aikin umuran.

KU KARANTA: Yadda ‘Yan-gaban goshin Buhari ke kokarin takawa Osinbajo burki

NAIJ.com ta ruwaito cewa, alkalin ya umurni hukumar ta EFCC da cewa ta tabbatar da ainihi dan majalisar wanda zai tsaya wa Bala kafin sake masa fasfo na kasa da kasa.

Mai shari’a ya dage al’amarin har zuwa watan Yuni 26 domin ci gaba da shari’ar.

Bala na fuskantar zargin almundahana da kudaden jama’a kimani biliyan 1.2.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon babban daraktan NNPC Andrew Yakubu a kotu kan zargin cin hanci da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel