Muna nan a kan bakarmu na kowani dan Kabilar Igbo ya koma ‘yankinsa – Kungiyar matasan Arewa

Muna nan a kan bakarmu na kowani dan Kabilar Igbo ya koma ‘yankinsa – Kungiyar matasan Arewa

- Kungiyar matasan Arewa ta ce duk da cewa gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi barazanar kama su da kai su kotu suna nan a kan bakan su

- Sun nemi duk wani dan kabilar Ibo da ya koma yankin sa cikin watanni uku

-Har ila yau sun nemi sananin matakin da El-Rufai ya dauka lokacin da aka kori Fulani daga yankin Kudu

Kungiyar matasan Arewa (Arewa Youth Consultative Forum, AYCF) ta ce duk da cewa gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai ya yi barazanar kama su da kai su kotu suna nan a kan bakan su na ba kabilar Ibo watanni uku su bar masu yankin su.

Kungiyar ta ce kowa ya koma yankin sa da zama don cin gashin kansa kawai.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar AbdulAziz Suleiman ya ce babu gudu ba ja da baya akan abin da suka shirya kuma suka sa a gaba.

Ya ce su basu nemi a yi tashin hankali ba, kawai dai suna so su nuna wa kabilar Ibo kuren su ne na cewa babu ruwansu da Najeriya. Saboda haka abu mafi sauki shine su kama gaban su.

KU KARANTA KUMA: Sarkin da ya fi kowa kudi a Najeriya (Kuma ba Sarkin Kano Sanusi II bane)

Game da barazanar kama su da gwamnan Kaduna yayi ikirarin yi, Suleiman yace El-Rufai na yin haka ne saboda son zuciya da siyasa.

“Wani mataki El-Rufai ya dauka lokacin da Inyamurai suka kori Fulani daga yankin su, me ya tabuka a kai?

“Yana ina lokacin da aka kashe ‘yan Arewa sama da guda 500 a yankin Ile-Ife, kawai don yana son ya tsaya takarar shugab ancin kasa sai ya nuna rashin kulawa ga mutanen sa sannan ya nuna fifiko a kan inyamurai."

NAIJ.com ta tuna cewa Kungiyar masu fafutukar neman kafa kasar Biyafara, ta yi kira ga ‘yan Kabilar Igbo da ke zaune a Arewacin kasar da su fara kokarin dawowa gida.

Shugaban kungiyar Uche Madu ya ce kowani dan Kabilar Igbo ya tattara kayansa da dawo su gina yankinsu na Biyafara.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila

Sabon ‘Dan wasan Manchester United zai fi kowa albashi a Kasar Ingila
NAIJ.com
Mailfire view pixel