Dalilin da ya sa rashawa ta yi kaka-gida a Najeriya -Ministar Kudi

Dalilin da ya sa rashawa ta yi kaka-gida a Najeriya -Ministar Kudi

- Kemi Adeosun, ta sanar da cewa rashawa ta yi kaka-gida a Najeriya ne sakamakon cewa kudaden gwamnati ba su da wahalar sacewa

- Ta ce gwamnatin tarayya na bakin kokarin ta wajen nemo dabarun hana sace-sacen kudaden kasa

Ministar kudi na Najeriya, Misis Kemi Adeosun, ta sanar da cewa rashawa ta yi kaka-gida a Najeriya ne sakamakon cewa kudaden gwamnati ba su da wahalar sacewa.

Da ta ke jawabi a wurin wani taro da Kwamitin sanya ido kan hana cin hanci da rashawa, wanda ofishin Shugaban Kasa ya shirya a ranar Talata, ta ce gwamnatin tarayya na bakin kokarin ta wajen nemo dabarun hana sace-sacen kudaden kasa.

KU KARANTA KUMA: Sarkin da ya fi kowa kudi a Najeriya (Kuma ba Sarkin Kano Sanusi II bane)

Taron ya kasance na hadin guiwa tare Ma’aikatar Shari’a ta kasa. Kemi ta kara da cewa, haka kuma gwamnati na daukar matakai na yadda ajiyar kudin sata a kasashen waje zai zama da matukar wahala ga duk wanda ya saci kudin daga kasar Najeriya.

Wata hanyar dakile yawan sace-sacen kudi ita ce bin dokoki da ka’idojin da doka suka tanada. Ta ce hakan yana da matukar tasiri wajen hana wawurar dukiyar kasar.

“Darasin da na koya a yanzu zama na Ministar Kudi ya nuna min, kuma ya sa ina da yakinin cewa wadannan matakai za su iya yiwuwa a nan Nijeriya. Don haka tilas ne mu tashi tsaye mu dauke su.

“A matsayin abin da na fahimta a zama na Ministar Kudi, kwato dukiyar da aka wawura abu ne mai kara min kaimi kuma ya na kara zaburar da ni. Sai dai kawai a ce abin zai dauki shekaru. Kun san kuma an ce daukar matakin hana aukuwar barna ya fi alfanu, a bisa neman maganin warkar da barna bayan ta auku.” Inji Kemi.

NAIJ.com ta kawo maku bidiyon ra'ayin jama'a game da kewar shugaban kasa Buhari wande ke birnin Landan yana jinya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel