Dattawan Arewa sun yi tur da batun raba kasa

Dattawan Arewa sun yi tur da batun raba kasa

- Dattawan Arewa sun yi Allah wadai da batun raba kasa

- Sun ce wannan kiraye-kirayen ba abune da zai haifar da da mai ido ba

- Har ila yau sun ba da shawarar a zauna a tattauna a tsakanin dattawan da ma matasan arewa domin nemo mafita

Wasu daga cikin ‘yan Majalisar Dattawa shiyar Arewa, sunyi Allah wadai da wa’adin da kungiyar matasan arewa suka baiwa ‘yan kabilar Igbo na su tattara komatsansu su bar yankin na Arewa a cikin watanni uku.

Da suke sharhi a kan wannan al’amari dattawan arewa sun nuna cewa wannna kiraye-kiraye da ya fara fitowa daga yankin kudu maso gabas, ba abune da zai haifar da da mai ido ba, domin yana iya kawo rabuwar kai d kiyayya mai karfin gaske a kasar.

KU KARANTA KUMA: Sarkin da ya fi kowa kudi a Najeriya (Kuma ba Sarkin Kano Sanusi II bane)

Madawakin Daura, Mustapha Bukar, Sanata mai wakiltar yankin Katsina ta arewa, ya ce kamata yayi ace duk abin da ake yi a zauna a tattauna a tsakanin manyan arewa da ma matasan domin nemo mafita. Wannan ne yasa aka kirkiro Majalisar Zartarwa ta gwamnoni da shugaban ‘kasa.

Dattawan Arewa sun yi tur da batun raba kasa

Mustapha Bukar, Sanata mai wakiltar yankin Katsina ta arewa, ya ce kamata yayi ace duk abin da ake yi a zauna a tattauna a tsakanin manyan arewa da ma matasan domin nemo mafita

Sanata Bukar, ya ja hankalin jami’an tsaro da su san irin matakin da zasu ‘dauka, haka zalika gwamnoni da wakilan tarayya da Majalisu su zauna su samar da matsera kan wannan al’amari.

A daya bangaren Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, daga jihar Kano ta Kudu, yayi sharhi a kan al’amarin inda yayi nuni kan cewa zama tare shine mafi alkhairi, saboda cewa dukkan al’umman Najeriya na bukatar junansu.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com, inda ta tambayi yan Najeriya ko sun ji kewan shugaban kasar su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel