Farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi zasu fado nan da sati biyu - Inji Ministan Noma

Farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi zasu fado nan da sati biyu - Inji Ministan Noma

- Ministan nona ya jaddada cewa farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi zasu fado cikin sati biyu masu zuwa

- Ministan ya ce an samu hashen fadowar farashin abinci ne bayan wani aikin sirri da komitin gwamnati ya gabatar

- Ogbeh ya ce hauhawan farashin abinci abune maras kyau ga mutanen da ba manoma ba

Ministan noma, Audu Ogbeh, wanda shine ke shugabantar hukumar da fadar shugaban kasa ta kafa domin samar da sassauci kan farashin abinci a kasa, ya tabbatar da cewar za'a samu sassaucin farashin kayayyakin abinci a cikin sati biyu masu zuwa.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Ogbeh ya ce wannan hasashe na zuwa ne bayan wani aikin sirri da komitin ya gabatar a kokarin gwamnatin tarayya na samarda wadataccen abinci cikin rahusa.

“Mun tattauna da manoma don samun mafita kan yadda za'a yi farashin abinci ya ragu. Gwamnati ta fadada ayyukanta ta fuskoki mabanbanta don ganin ta karfafa harkar noma abinci ya wadatu.”

Farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi zasu fado nan da sati biyu - Inji Ministan Noma.

Kasuwan doya a mile 12 da ke Legas

KU KARANTA: Darajar Naira: Dala na kara rushewa a kasuwar canji

Ministan ya cigaba da cewar : "Nayi amanan cewar hauhawan farashin abinci abune maras kyau ga mutanen da ba manoma ba, amma abune mai kyau ga kasa kasancewar mutane da yawa zasu koma noma. A karshe kuma za'a sami wadataccen abincin da zai sa farashi yayi faduwar dole"

Farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi zasu fado nan da sati biyu - Inji Ministan Noma.

Ministan noma, Audu Ogbeh ya ce farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi zasu fado nan da sati biyu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel