Darajar Naira: Dala na kara rushewa a kasuwar canji

Darajar Naira: Dala na kara rushewa a kasuwar canji

– Babban bankin Najeriya zai fara saidawa jirage Dalar Amurka

– Haka kuma za a rika saidawa masu jigilar mai da manoma Dalar

– Babban bankin kasar na cigaba da sakin Daloli a kasuwa

Kun ji cewa Dalar Amurka na rage daraja a kasuwar canji

Yanzu ma dai Dalar tana kan N366 ne

Hakan dai na nuna cewa abubuwa na dan kara kyau

Darajar Naira: Dala na kara rushewa a kasuwar canji

Babban bankin Najeriya zai fara saidawa manoma Dala

Jiya kun ji cewa bisa dukkan alamu dai ana shirin kai ga ci a tsarin na CBN don kuwa Naira na ta kara tashi sannu-a-hankali. Kuma ana sa rai Nairar ta kara daraja nan gaba yayin da CBN ke cigaba da dumbuza Daloli a kasuwa.

KU KARANTA: Neman Duniya: Dubi abin da aka kama wani yayi

Darajar Naira: Dala na kara rushewa a kasuwar canji

Darajar Naira na yin sama a kasuwar canji

Yanzu haka dai za a fara saidawa kamfanin jirgin sama Daloli domin a samu sauki. Haka kuma za a rika saida Dalolin ga ‘yan kasuwa masu harkar mai da kuma manyan manoma kai tsaye. Hakan dai zai yi maganin cunkoson da ake samu wajen neman Dalar.

Yanzu dai ana saida Dalar a kasuwar canji ne a kan N366. Bankuna kuma na saidawa kan 305.60. A makon jiya an saida Dalar Amurka ne a kan N382.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ba haka ake so ba: Miji bai kai matar sa albashi ba [Bidiyo]

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel