Yadda ‘Yan-gaban goshin Buhari ke kokarin takawa Osinbajo burki

Yadda ‘Yan-gaban goshin Buhari ke kokarin takawa Osinbajo burki

– Akwai rade-radin cewa wasu Ministocin Buhari na kokarin hana Osinbajo aiki

– Daga ciki wadanda aka kira sunan su akwai Sanata Hadi Sirika

– Ana zargin Abba Kyari da yin duk wani kutun-kutun na danne Yemi Osinbajo

Sahara Reporters ta zargi Abba Kyari da kokarin murkushe Farfesa Osinbajo

Yemi Osinbajo ne dai ke rike da kasar tun bayan tafiyar Shugaba Buhari

Ana kuma zargin wasu Ministoci da hana Mukaddashin aikin sa

Abba Kyari, Shugaba Buhari da Osinbajo

Ana zargin Abba Kyari da yunkurin danne Osinbajo

A wani labari da Jaridar Sahara Reporters ta fitar akwai kishin-kishin din cewa wasu Ministocin Buhari irin su Sanata Hadi Sirika na kokarin hana Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo aikin sa.

KU KARANTA: Zargin Boko Haram: Namadi Sambo ya san da maganar Inji Sanata Ndume

Malam Abba Kyari

Abba Kyari na kokarin murkushe Farfesa Osinbajo Inji Sahara Reporters

A cewar su an yi wani taro a Birnin Landan duk da Shugaban kasar Muhammadu Buhari bai sani ba. Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari ne dai da wasu ma’aikatan shugaban kasar ke kokarin hana Yemi Osinbajo aikin sa kamar yadda doka ta tanada.

A bayan mun ji labari cewa ba mamaki an dan buga wani aringizo ne ko an yi wata ‘yar badakala a cikin kasafin kudin bana. Don haka ne ma Ministocin kasar su ka nemi cewa ka da Mukaddashin Shugaban kasa ya sa hannun sa a kan kasafin bana tukun.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ko 'Yan Najeriya na kewar Shugaba Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel