Biafra: Yan kabilar Igbo ba zasu taba nasara kan wata manufa ba saboda basu da hadin kai - Pete Edochie

Biafra: Yan kabilar Igbo ba zasu taba nasara kan wata manufa ba saboda basu da hadin kai - Pete Edochie

Tsohon jarumin Nollywood, Pete Edochie, yayi bayanin cewa yan kabilar Igbo ba zasu taba nasara kan wata manufa ba saboda basu da hadin kai.

Pete Edochie yace Igbo a waste suke, babu wata takamamman manufa, kuma babu wata manufa da zai hada kansu face al’adunsu na gargajiya.

Game da cewar tsohon jarumin, yawancin yan kabilar Igbo basu iya yarensu yayinda yayi kira ga shugabannin Igbo su nemi hanyar hada kawunan mutanensu.

Edochie, ya bayyanawa manema labarai cewa, “Akwai abubuwa da dama da ke sani hawaye. daya daga cikinsu shine Igbo a waste suke, babu hadin kai.”

“Idan ka duba Igbo sosai, zaka lura cewa ba zasu iya fada tare ba. Babu wani yakin neman yancin da zai hada kan mutanen Igbo.”

Biafra: Yan kabilar Igbo ba zasu taba nasara kan wata manufa ba saboda basu da hadin kai - Pete Edochie

Biafra: Yan kabilar Igbo ba zasu taba nasara kan wata manufa ba saboda basu da hadin kai - Pete Edochie

“idan ka lura, zaka gano cewa a fadin Najeriya ga baki daya, mutanen Igbo sunfi kowa sha’awan yaren turanci.”

“Dan bahaushe ba zai gashe da mahaifinsa da turanci ba. Bayarabe ba zai gaishe da mahaifinsa da turanci ba.”

KU KARANTA: Yan kasuwan canji sun tafka mumunar asara

“Amma inyamuri zai ce ‘good morning sir’ a maimakon amfani da yarensa. abin takaici ne cewa yaren Igbo na karewa kuma babu wanda ya damu.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel