Dubun wani ɗan yankan kai ta cika a jihar Delta

Dubun wani ɗan yankan kai ta cika a jihar Delta

- Yansanda sun kama mutumin dake fatauci sassan jikin mutum cikin jarka

- Yansandan sun kama mutumin ne akan hanyarsa ta zuwa Legas daga Delta

A ranar Lahadi 4 ga watan Yuni yansandan jihar Delta suka cika hannu da wani mutum mai shekaru 45 Felix Nnalu dauke da kawuna da sauran sassan jikin mutum, kamar yadda Sahara Reporters at ruwaito.

Yansandan sun kama Felix ne a yankin Abavo na jihar Delta, inda ya zuba sassan jikkunan mutane da dama cikin wasu jarakuna daya zuba ma wasu sinadarai domin hana sassan lalacewa da wuri.

KU KARANTA: Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito cewa Felix ya boye jarakunan ne cikin wasu buhunan garri guda biyu inda ya nufi jihar Legas domin cinikin sassana, kamar yadda kaakakin rundunar yansandan Andrew Aniamaka ya bayyana.

Dubun wani ɗan yankan kai ta cika a jihar Delta

Dan yankan kai

Kaakakin yace jami’ansu sun kama mutumin ne da misalin karfe 10:30 na safiyar ranar Lahadin data gabata, inda ya bayyana mutumin a matsayin daya daga cikin yan yankan kai da suka addabi jihar.

“Kamen na da nasaba da wani bincike da muke gudanarwa na wasu mutane da aka sace sakamakon rikicin wasu fulotan filaye tsakanin al’ummomin Umuebu/Amai/Eziokpo /Obiaruku dake yankin Ukwuani.

“Mun kama mutumin dauke da buhunan gari guda 2, jarakuna lita 4 guda 2 dake dauke da sassan jikunan mutane. Zamu cigaba da bincike don gani sauran abokan aikin nasa.” inji Kaakakin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel