Jami'an 'yan sanda a jihar Neja Sun fara rufe gidajen siyar da giya

Jami'an 'yan sanda a jihar Neja Sun fara rufe gidajen siyar da giya

- Jami’an ‘yan sandan jihar Neja sun fara daukar matakin rufe gidajen siyar da giya da sauran kayan shaye shaye

- Jami'an 'yan sanda sun karbe duk wani lasisi na gidan giya tare da rufe gidajen giya musamman wanda ke cikin al'umma

- Kayan shaye shaye dai na lalata da 'yan mata harda matan aure

- Jihar Neja ta nada tsarin dokakin shari'ar musulunci da ya haramta siyar da kayan barasa da gidajen giya a fadin jihar

A kokarin su na magance matsalar shaye shaye da aikata aiyukan sabon Allah musamman a wannan wata na azumi, jami'an hukumar 'yan sandan garin Kontagora dake jihar Neja sun fara daukar matakin rufe gidajen siyar da giya da sauran kayan shaye shaye cikin garin.

Daya daga cikin wuraren da jami'an 'yan sandan suka samu nasarar rufewa ya hada da wani shahararren gidan siyar da kayan barasa na kali dake Tudun-Wada Kontagora, wanda yayi kaurin suna wurin siyar da kayan shaye shaye da lalata da karuwai da 'yan mata harda matan aure, hakazalika jami'an 'yan sandar sun dauki matakin karbe duk wani lasisi na gidan giya tare da rufe gidan musamman wanda ke cikin al'umma.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, daukar wannan mataki dai ya biyo bayan korafe korafen da al'umma suke ta yine akan yawaitar gidajen siyar da giya wanda ya kasance matattarar aikata laifuffukan sabon Allah, wanda hakan ke lalata tarbiyar al'umma musamman samari da 'yan mata, duk da kasancewar Jihar ta Neja ta nada tsarin dokakin shari'ar musulunci da ya haramta siyar da kayan barasa a gidajen giya a fadin jihar wanda tsohon gwamna marigayi Abdulkadir Abubakar Kure ya kaddamar a shekarar 2001.

Jami'an 'yan sanda a jihar Neja Sun fara rufe gidajen siyar da giya

Jihar Neja ta nada tsarin dokakin shari'ar musulunci da ya haramta siyar da kayan barasa a gidajen giya

KU KARANTA: Gwamnatin El-Rufa’I ta yaudare mu – Matasan APC

Al'umma da dama ne suka nuna gamsuwar su tare da jinjina ga wannan mataki da jami'an 'yan sandan suka dauka, sannan sunyi kira ga sauran jihohin Najeriya musamman na yankin Arewa da su hanzarta daukar irin wannan mataki domin magance matsalar ta barbarewar tarbiya da aikata ayyukan sabon Allah dake barazana ga yankin na Arewa wanda galibin masu wadannan gidajen giya ba al'ummar Arewa bane.

Sun kuma yi kira da cewar ya zama wajibi ga shugabanni da jami'an tsaro da sauran al’umma da a hada karfi wurin kawar da wadannan munanan dabi'u a wannan yanki na Arewa dake da kyawawan al'adu da addinai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Rikicin kudancin jihar Kaduna kashi na 2

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel