Rashin aiki ya karu a Nigeria da kashi 2

Rashin aiki ya karu a Nigeria da kashi 2

- Kididdiga na nuna cewa yawan marasa aikin yi a Najeriya ya karu da fiye da kashi 2 cikin 100 a rubu'in karshe na shekarar bara

- Kimani mutane miliyan 11.5 ne adadin marasa aikin yi a Najeriya

- Hukumar kula da kididdiga ta ce matsalar rashin aikin yi tafi shafuwar matasa

Hukumar kula da kididdiga ta Najeriya ta ce yawan marasa aikin yi a kasar ya karu da fiye da kashi 2 cikin 100 a rubu'in karshe na shekarar bara.

Wannan na nufin adadin marasa aiki a kasar ya kai mutane miliyan 11.5, abin da ke daidai da kashi 14% na mutanen da ke iya aiki a kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, alkaluman da hukumar ta National Bureau of Statistics ta fitar sun nuna cewa matsalar rashin aikin tafi shafuwar matasa ne wadanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 34.

Haka ma ko baya ga rashin aiki sam-sam, akwai kuma matsalar samun ayukkan da ba su dace da kwarewa ko matsayin wasu ma'aikatan ba wadda ta ce fiye da kashi 21% na masu ayukkan yi a kasar ne ke fama da irin wannan matsalar.

KU KARANTA: Ashe Shugaba Jonathan ne ya dagargaza tattalin arzikin kasar nan

Sai dai rahoton bai bayyana dalilan da suka kawo karuwar rashin ayyukan a kasar ba, amma dai a bara din ne kasar ta shiga cikin halin karayar arziki mafi muni cikin shekaru 20 sakamakon faduwar farashin danyen mai wanda shi ne babbar hanyarta ta samun kudaden shiga.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Zanga-zangar lumana kan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel