Aure na da matukar muhimmaci wajen kara lafiya - Rahoto

Aure na da matukar muhimmaci wajen kara lafiya - Rahoto

- Da alamu aure na da matuƙar muhimmanci wajen inganta lafiya, da tsawon rai idan kana da wasu larurori masu alaƙa da ciwon zuciya kamar yadda wasu masu bincike suka gano.

- Nazarin wanda masana ilmin kimiyya a Burtaniya suka gudanar ya nuna cewa aure, abu ne mai alfanu ga zuciya.

An shafe tsawon shekara 13 ana gudanar da binciken a kan fiye da mutum dubu 900 masu larurorin da ke da alaƙa da ciwon zuciya, ya gano cewa ma'auratan da ke da yawan maiƙo a jiki sun fi yiwuwar zama a raye da kashi sittin cikin 100 idan an kwatanta da gwagware.

Haka ma labarin yake ga ma'auratan da ke da ciwon suga da hawan jini.

NAIJ.com ta samu labarin cewa masu binciken sun yi imani, abokan aure ka iya ƙarfafa gwiwar junansu ta yadda za su ci gaba da zama garau da lafiya. Ko da yake ba su iya tabbatar da hakan ba, Dr Paul da abokan aikinsa da suka gudanar da wannan bincike, sun riga sun nuna cewa aure na da alaka da samun waraka daga ciwon zuciya.

Aure na da matukar muhimmaci wajen kara lafiya - Rahoto

Aure na da matukar muhimmaci wajen kara lafiya - Rahoto

Binciken baya-bayan nan da aka gabatar a taron ƙungiyar ƙwararru kan cutukan da ke da alaka da bugun zuciya ta Burtaniya, inda ya yi hasashe kan dalilan da ka iya janyo faruwar haka.

Sun yi ittifaƙin cewa aure yakan taimaka wajen kare ma'aurata daga abubuwan da ke haifar da barazanar kamuwa da ciwon zuciya ciki har da maiƙon da ake samu a cikin jini da kuma cutar hawan jini.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel