Shirin N-Power: Osinbajo ya bada umurnin bude shafin daukan aikin ranan 17 ga watan Yuni

Shirin N-Power: Osinbajo ya bada umurnin bude shafin daukan aikin ranan 17 ga watan Yuni

Mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayar da umurnin cewa a bude shafin yanar gizon shirin dauka aikin matasa na N-Power ranan 17 ga Yuni.

Karamar ministan kasafin kudi, Zainab Shamsuna Ahmed ne ta bayyana hakan ranan Talata a Abuja.

Zainab tace gwamnatin tarayya zata tabbatar da cewa shirin ta dauki ma’aikata da dama a wannan shekaran kuma tana jawo hankalin matasa suyi rijista.

Tace shirin taimakon jama’a na gwamnatin Najeriya wato National Social Investment Programme (N-SIP), ta karfara yan Najeriya 1.6million zuwa yanzu.

Shirin N-Power: Osinbajo ya bada umurnin bude shafin daukan aikin ranan 17 ga watan Yuni

Shirin N-Power: Osinbajo ya bada umurnin bude shafin daukan aikin ranan 17 ga watan Yuni

“Misali, a shirin N-Power an dauki mutane 200,000, yakamata mu karashi zuwa 500,000 a 2017.”

“Wannan wani dama ne na N-Power domin samun aiki. Wannan zai taimaka wajen samun kudin fara kasuwanci.”

KU KARANTA: Masari Azzalumin mutum ne - Shema

“Ba’a fara tura mutane da kuma sakin kudi ba sai a watan Oktoba 201; shi yasa muke sin mu tabbatar da cewa an shirya sosai.”

“Muna son mu tabbatar da cewa wadanda aka dauka na da asusun bankin had da BVN; muna bukatan mabukata ba yaran masu kudi ba.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel