Arzikin man fetur ɗin Najeriya, na Arewa ne – Inji Usman Bugaje

Arzikin man fetur ɗin Najeriya, na Arewa ne – Inji Usman Bugaje

- Bugaje yayi ikirarin arzikin man fetur da ake takama da shi mallakin yankin Arewa ne.

- Bugaje sakamakon girman Arewa aka samu man fetur

Wani masani kuma daya daga cikin shuwagabannin kungiyar dattawan Arewa, Alhaji Usman Bugaje yayi ikirarin cewar gaba daya arzikin man fetur da ake takama da shi a kasar nan mallakin yankin Arewa ne.

Jaridar Daily Post ta ruwaito Usman Bugaje yana bayyana haka ne yayin wata ganawar tattaunawa da yayi da shuwagabannin Arewa, inda yace babu wata jihad a ta isa tayi ikirarin samar da man fetur a kasar nan.

KU KARANTA: Zul waja haini: Yaro mai fuska 2 ya cika shekaru 13 (Hotuna)

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Bugaje ya danganta arzikin man fetur ga Arewa saboda fadin girman kasa da Allah ya wadata yankin da shi, wanda a cewarsa wannan itace manuniyar cewa arzikin ma fetur na Arewa ne.

Arzikin man fetur ɗin Najeriya, na Arewa ne – Inji Usman Bugaje

Mahakar mai na ruwa

“Babu jihar da za tayi ikirarin samar da mai a Najeriya, Najeriya ce kadai keda ikon yin wannan ikirarin, idan ma akwai wani bangare dake da ikon yin wannan ikirarin itace Arewa, saboda girman fadin kasar ta ne ya sanya Najeriya ta samu mallakan fadin sarari a ruwa.” Inji Bugaje.

Bugaje yace kamar yadda majalisar dinkin duniya ta tanada, fadin kasa, shine fadin ruwa, inda yace giran kasa da Arewa ke da shi ne ya samar ma Najeriya sararin ruwan da ake hako mai.

Arzikin man fetur ɗin Najeriya, na Arewa ne – Inji Usman Bugaje

Usman Bugaje

“Sakamakon kashi 72 na kasar Najeriya na Arewa, wannan shine dalilin dayasa aka samu mil 200 na ruwan Najeriya, da ha rake diban mai a ciki. Don haka takamar da suke yi cewa mai nasu ne, ba haka bane.

“Idan ma wani zai yi ikirarin mallakan mai, ai Arewa ne tafi dacewa tayi hakan, don haka babu wata jiha mai fitar da mai, Najeriya kadai ke mallakan mai.” Inji Usman Bugaje

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Makafi 4 yan gida daya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel