Umarnin samarin Arewa na Ibo su fice daga Arewa: Samarin Ibo suma sun mayar da martani

Umarnin samarin Arewa na Ibo su fice daga Arewa: Samarin Ibo suma sun mayar da martani

- Ba'a fiye ga maciji ba, a tsakanin kabilun Najeriya a lokutan siyasa

- Kalaman samarin arewa na kara tunzura 'yan kabilar Ibo

- Hukumomi sun zuba wa abun ido

Har ya zuwa yanzu dai hukumomi basu mai da hankali kan batun bamgaranci dake ta yamadidi tsakanin samarin kasar nan ba.

Ana yawan kama wadanda suke batun ballewa a kulle in sun fito daga kudancin kasar nan, amma shiru kake ji babu wanda aka kama cikin samarin da suka baiwa kabilar Ibo wa'adin makonni ukku su fice su bar Arewacin kasar.

Umarnin samarin Arewa na Ibo su fice daga Arewa: Samarin Ibo suma sun mayar da martani

Umarnin samarin Arewa na Ibo su fice daga Arewa: Samarin Ibo suma sun mayar da martani

Amma su kuma samarin kabilar Ibo din sun mayar da martani, inda suka ce yarinta ce samarin arewar keyi, na barazana ga samari daga bangaren kabilar Ibo, sun kuma ce ai su basu tsoron yaki.

IYM Evang, shugaban samarin kudun ya fadi hakan ne a yau da safe bayan labari da ya fito jiya daga arewa cewa jama'ar kabilar kudu su fice daga arewar.

'Ai mu munfi so ku rubutawa majalisar Najeriya kuce kuna so a saka kwanan watan zaben raba gardama kan ko muma muna son ballewa ko a'a.' Ya kara da cewa.

Yayi zargin samarin arewar da son su kori kabilun kudu domin su gaje dumbin dukiyar su da kadarorinsu da ke yankin.

'A maimakon korar jama'a, ku ci gadon dukiyarsu, ai rafarandan zaku sa majalisa ta yi, kowa ya rabu a huta, domin wannan kira ga yaki bazai bamu tsoro ba, duk da cewa kuna kallon wadanda suke cikinku ne kawai da mugun nufi.' Ya kara da cewa.

Wannan dai na nufin musayar zafafan kalaman da wasu samarin keyi ya zama wani abin tinkaho ga wasu kabilun Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel