Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

- Yan bindiga sun afka wa kabarin babban malamin addinin shi’a, Khomeini

- Yan kunar bakin wake sun kai hari majalisar dokokin kasar Iran

Wasu yan bindiga sun afka wa kabarin babban malamin addinin shi’a, kuma jagoran jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Khomeini tare da majalisar dokokin kasar Iran, duk a babban birnin kasar Iran, Tehran, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito cewa lamarin ya rutsa da mutane da dama, inda ta ruwaito an yi ta jin karar harbe-harbe daga na'urorin amsa kuwwa dake farfajiyar majalisar dokokin kasa.

KU KARANTA: Ramadana: Rundunar Yansanda ta hana Tashe a Kano

Sai dai wasu rahotonni sun bayyana cewar an kashe daya daga masu gadin majalisar yayin harin, haka zalika mutane da dama sun da harin ya rutsa dasu a hubbaren Ayatollahi sun jikkata.

Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

Kabarin Ayatollahi Khomeini

An ruwaito aga cikin maharan da suka kai harin akwai dan kunar bakin wake daya, sai 'yan bindiga guda uku. Sai dai daya daga cikin maharan ya mutu sakamakon tashin bam din da yayi a gaban wani banki dake kusa da hubbaren, kamar yadda gwamnan Tehran ya shaida.

Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

Majalisar Iran

Hakazalika an bayyana cewar daya daga cikin yan bindigan ya mutu sakamakon musayar wuta da jami'an tsaro.

A wani hannun kuma, kungiyar ta’addanci ta ISIS ta sanar da daukan alhakin kai harin, wanda ake tunanin wanda ya kai harin kunar bakin waken mace ce ma, kuma tana sanye ne da bakin tufafi,

Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

Hayakin harin

“Mayakan ISIS ne suka kai hari a kabarin Khomeini da majalisar dokokin Iran a Tehran, kuna ganin zamu tafi ne? muna nan da ikon Allah.” Inji ISIS.

Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

Ana tseratar da mutane

Kungiyar ISIS ta ɗauki alhakin kai harin ýan bindiga a kabarin Ayatollahi Khomeini

Jami'in Dansanda

Ga bidiyon a nan:

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shugaba Buhari zai dawo

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel