Labari yanzu-yanzu: Majalisar Dattijai ta amince a nada dan shekara 82 a matsayin Jakada

Labari yanzu-yanzu: Majalisar Dattijai ta amince a nada dan shekara 82 a matsayin Jakada

- An nada tsoho dan shekara 82 jakadan Najeriya, wanda ya fito daga jihar Imo

- Hukumar tsaro ta farin kaya ta bada mummunan rahoto a kansa amma kwamitin majalisar ya wanke shi

- A yanzu dai an kusa kammala nade-naden mukamai a gwamnatin APC, shekaru biyu da rabi da cin su zabe

Jastis mai ritaya Sylvanus Nsofor daga jihar Imo ya sami yarjewar majalisar dattijai kan ko a nada shi jakadan Najeriya ko kuma a'a.

A baya dai majalisar ta ki yarje masa bayan rahoton hukumar DSS da ya sakala masa tabo. Sai dai sabon wanki da kwamitin majalisar yayi masa ya fitar dashi subul.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta biya masu fallasa kudin sata Naira miliyan 375.8

Labari yanzu-yanzu: Majalisar Dattijai ta amince a nada dan shekara 82 a matsayin Ambasada

Labari yanzu-yanzu: Majalisar Dattijai ta amince a nada dan shekara 82 a matsayin Ambasada

Sauran jerin sunayen da majalisar ta karba daga fadar shugaban kasa suma sun sami yarjewar mafi yawa daga dattijan. Wannan sanarwar ta fito ne yanzu yanzu daga hannun shafin majalisar ta twitter, @NGRSenate.

'Majalisa ta zartas da amincewa ga mutum ukku da aka turo don tantancewa su zama jakadun Najeriya' Sanarwar ta wallafa.

Har yanzu dai ba'a gama nade-nade a gwamnatin Buhari ba, duk da wa'adin mulkin zai kare nan da shekara daya da doriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

NAIJ.com ta kawo maku nasarorin shugaba Buhari cikin shekaru biyu

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel