Gwamnatin tarayya ta biya masu fallasa kudin sata Naira miliyan 375.8

Gwamnatin tarayya ta biya masu fallasa kudin sata Naira miliyan 375.8

- Gwamnatin tarayyan Najeriya ta ware zunzurutun kudi har Naira miliyan 375.8 don biyan masu busa uzur a kan kudaden

- Mutane 20 suka amfana daga wannan shiri a karo na farko

- Dukka wannan na cikin kokari da gwamnatin shugaba Buhari ke yi na yaki da cin hanci da rashawa

Gwamnatin tarayyan Najeriya ta ware zunzurutun kudi har Naira miliyan 375.8 don biyan masu busa uzur a kan kudaden sata 20 da suka taimaka wa hukumomin kasar wajan gano Naira Biliyan 11.6.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar kudi na tarayya ta tabbatar da sakin kudaden ta ce, a karon farko kenan da ake biyan mutane karkashin wannan sabon tsari na fallasa kudaden satar.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ba mu saki Dasuki da Zakzaky ba Inji Gwamnatin Tarayya

Sai dai gwamnati ba ta bada bayani game da mutanen da suka amfana daga kudaden ba saboda dalilai na tsaro.

Ma’aikatar ta ce, matakin biyan ya nuna irin yadda gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta mayar da hankali don cika alkawarinta ga masu fallasar, wadda ke da matukar muhimmanci wajen yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar Najeriya.

Gwamnati na bai wa masu fallasar akalla kashi biyar cikin dari (5%) na kudaden da suka bayar da bayanansu kuma aka gano su, amma an tanadi hukuncin dauri a gidan yari kan duk wanda ya fallasa bayanai na karya.

.NAIJ.com ta kawo maku bidiyon gangamin hukumar EFCC kan yaki da rashawa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel