Gwamnatin El-Rufa’I ta yaudare mu – Matasan APC

Gwamnatin El-Rufa’I ta yaudare mu – Matasan APC

Matasan kungiyar yakin neman zaben El-Rufai a 2019, a ranan Talata, a jihar Kaduna sun afka majalisar dokokin jihar domin zanga-zanga kan rashin cika alkawuran gwamnatin na sama musu aikin yi.

Matasa masu zanga-zangan sun taru ne a a gaban Lugard Hall inda suke cewa “Ba zamu yi APC a 2019 ba”, sun tare babban hanyar shiga da fitan majalisar dokokin jihar.

Sakataren kungiyar, Sadeeq Shuaibu, yayinda yake magana da manema labarai yace shi gwamna El-Rufai na iyakan kokarinsa wajen ganin cewa anyi da matasan jihar amma ma’aikatansa ne suke yi masa zagon kasa.

Yace: Mai girma gwamnan yac zai mayar da mutuncin jihar Kaduna, amma wadanda zasu taimaka masa wajen hakan ne ke karerayi da yaudaran matasa.

Gwamnatin El-Rufa’I ta yaudare mu – Matasan APC

Gwamnatin El-Rufa’I ta yaudare mu – Matasan APC

“Duk da cewa wasu matasan da sukayi musharaka wajen yakin neman zaben na da aikin traffic wasu kuma na kasuwanci, amma wadanda gwamna El-Rufai ya dauka aiki ne ke kokarin ajiye matasa a gefe.”

Yawancinmu da kuke gani muna zanga-zangan ne mun sha tsegumi lokacin zaben wannan gwamnati, amma gamu nan babu aiki, ba taimako.

KU KARANTA:

“Muna son mu sanar da gwamnan jihar Kaduna cewa duk wani shirin da yake wa matasa bai isa garesu ba , abokan aikinsa en ke kaiwa iyalansu da danginsu."

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel