Majiyoyi sun bayyana gaskiyar halin da lafiyar Zakzaky ke ciki

Majiyoyi sun bayyana gaskiyar halin da lafiyar Zakzaky ke ciki

- Lafiyar El-Zakzaky ya kasance abun kula ga mabiyansa tun bayan da gwamnatin Najeriya ta tsare shi

- Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa shugaban kungiyar Shi’a na cikin koshin lafiya

- Har ila yau majiyoyin sun kawo karshen dukkan jita-jita dake yawo na cewa ya mutu

Ana ta samun tashe-tashen hankula kan halin da lafiyar kamemen shugaban kungiyar Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ke ciki.

A yayin da aka shiga watan Ramadan ana ta yada jita-jita kan lafiyarsa harma da zargin cewa ya mutu, wanda hakan ya haddasa tsoro a tsakanin mabiyan sa da ma sauran Musulmai.

A cewar jaridar Vanguard, wata majiyar tsaro mai karfi ta fada ma PRNigeria a Abuja cewa El-Zakzaky na raye, cikin koshin lafiya sannan kuma ya yi watsi da rade-radin mutu a matsayin aikin masu fasadi, wadanda ke son haddasa tsoro da tashin hankali a gari.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa ba mu saki Dasuki da Zakzaky ba Inji Gwamnatin Tarayya

Jami’in ya kara da cewa kungiyar dake kula da al’amuran musulmai na Najeriya (NSCIA) da ma sauran manyan shugabannin musulunci, hadi da iyalansa sun sha kai ma shugaban kungiyar Shia, Sheikh Ibrahim Zakzaky ziyara a baya a inda yake tsare a Abuja don tabbatar dairin wannan jita-jitan na mutuwa.

NAIJ.com ta tuna cewa Sheikh Zakzaky na tsare a hannun hukumar DSS tun bayan kama shi da hukumar sojin Najeriya ta yi a ranar 14 ga watan Disamba na 2015.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel