'Dole Buhari ya rattaba hannu a kudirin kasafin kudin bana kafin watan nan ya kare'

'Dole Buhari ya rattaba hannu a kudirin kasafin kudin bana kafin watan nan ya kare'

- Sai da rattababben kasafin kudi gwamnati zata iya kashe kudi a doka

- Kasafin kudin bana bai sami rattabawar hannun shugaba Buhari ba

- An sami rabin shekara a cikin sabuwar shekarar 2017

A Najeriya, an sami tsaiko sau da dama idan aka zo batun kasafin kudi da yadda za'a tafiyar da kundin sa. A baya, rashin lafiyar shugaba Ummaru Yar'aduwa ta kawo tsaiko da dambarwa kan yadda zai iya rattaba hannu bayan yana jinya.

To a bana ma dai hakan take, inda ake jiran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kas kasafin kudin bana duka da cewa har anci rabin shekarar.

Amma mataimakin bulaliyar majalisa ya ce akwai sauran lokaci, tun da kasafin bara ma ba'a gama cinye shi ba tukunna, wanda a doka sai watan Mayu aka gama cinye shi.

'Dole Buhari ya rattaba hannu a kudirin kasafin kudin bana kafin watan nan ya kare'

'Dole Buhari ya rattaba hannu a kudirin kasafin kudin bana kafin watan nan ya kare'

Pally Iriase, bulaliyar majalisa yace shugaba Buhari na da makonni ne kawai zuwa karshen watan nan na Yuni, kafin wa'adin kudin ya cika.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta biya masu fallasa kudin sata Naira miliyan 375.8

'Shugaba Buhari yana da sauran lokaci, yana da kusan kwana 30, amma dole ne ya rattaba hannu a wannan lokacin.' Ya kara da cewa.

In dai ba saka hannu akayi a sabon kasafin ba, ya haramta a sake kashe kudi a gwamnatance. Sai dai komai ya tsaya chak, a irin abinda ake kira govt shutdown a turance.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel