Ministan Buhari ya nemi gafarar Sheikh Isah Pantami

Ministan Buhari ya nemi gafarar Sheikh Isah Pantami

- Solomon Dalung ya nemi gafarar babban malami, Isah Pantami

- Minista Dalung ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar

Ministan wasanni da harkokin matasa, Solomon Dalung ya nemi gafarar babban malami, kuma shugaban hukumar inganta kimiyya da fasaha, Malam Isah Ali Pantami, sakamakon raddin daya mayar ma Pantami kan tayin shiga addinin Musulunci da yayi masa.

Minista Dalung ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a shafinsa na Facebook, kamar yadda NAIJ.com ta gani, inda yace:

KU KARANTA: Gwamna Ganduje ya kawo ƙarshen rikici tsakanin Abdulmuminu da Doguwa

“Inda yace ina neman afuwan Malam Isah Pantami da duk wanda bai ji dadin martanin da mayar ba bayan lamarin daya faru a masallacin Anoor dake Wuse, Abuja. ni dan Adam ne kamar kowa, kuma ajizi ne nI.

Ministan Buhari ya nemi gafarar Sheikh Isah Pantami

Dalung da Sheikh Isah Pantami

“Ga duk masoya na, suma ina neman gafarar su, sa’annan na doge ma wadanda suka bani shawarar inyi tunanin abinda nayi, Allah ya saka muku da alheri. Manufata itace samar da kyakkyawar fahimta tsakanin addinan biyu.

“Mai yiyuwa ne ban bi hanyar data dace ba, amma manufata tsarkakakkiya ce, a matsayina na Kirista, ban gamsu da yadda aka kirani zuwa ga musulunci ba, amma na fahimci hakan ba wani abu bane a Musulunci

“Ina tabbatar ma Pantami cewar ina ganin girmansa sosai, kuma muna da kamanceceniya da dama, don haka mu cigaba da kokarin kawo zaman lafiya mai daurewa a kasar nan." Inji Solomon Dalung.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wani abin tausayi.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja

Tirkashi! Har yanzu akwai al'ummomin da ke riko da al'adan kashe tagwaye a Abuja
NAIJ.com
Mailfire view pixel