Gwamna Ganduje ya kawo ƙarshen rikici tsakanin Abdulmuminu da Doguwa (Hotuna)

Gwamna Ganduje ya kawo ƙarshen rikici tsakanin Abdulmuminu da Doguwa (Hotuna)

- Zaman doya da manja tsakanin Abdulmuminu Kofa da Alhassan Doguwa yazo ƙarshe

- Gwamna Ganduje ne yayi wannan sulhu tsakanin yan majalisun biyu

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yayi ruwa yayi tsaki don kawo sulhu tsakanin wasu jiga jiga jam’iyyar APC a jihar Kano da basa ga maciji, Ado Al-Hassan Doguwa da Abdulmuminu Jibrin.

Ado Al-Hassan Doguwa shine dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Doguwa da Tudun-wada, sa’annan shine mai tsawatarwa a majalisar tarayya, yayinda Abdulmuminu Jibrin Kofa ke wakiltar mazabar Kiru da Bebeji.

KU KARANTA: Ba ni shakkar kowa a Najeriya – Al-Mustapha

Sulhun na gwamna Ganduje ya faru ne a ranar Litinin 6 ga watan Yuni, a filin tashin jirgi na Aminu Kano, inda gwamnan ya gayyaci mataimakin gwamna Farfesa Hafiz, sakataren gwamnati Usman Alhaji da shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Abbas don zaman shaidu.

Gwamna Ganduje ya kawo ƙarshen rikici tsakanin Abdulmuminu da Doguwa (Hotuna)

Abdulmuminu da Doguwa

NAIJ.com ta ruwaito yan majalisun biyu sun kwashe wata da watanni ba sa shiri tun bayan dakatar da Abdulmuminu Jibrin da aka yi daga halartan zaman majalisa na stawo shekara guda, sakamakon hakan ya janyo rashin jituwa a jam'iyyar APC ta jihar Kano tsakanin magoya bayansu.

Da wannan sulhu ake sa ran zaman doya da manja tsakanin Abdulmuminu Kofa da Alhassan Doguwa ya kawo karshe, wata kila hakan yayi sanadiyyar mayar da shi cigaba da halartan zaman majalisa.

Ga sauran hotunan:

Gwamna Ganduje ya kawo ƙarshen rikici tsakanin Abdulmuminu da Doguwa (Hotuna)

Gwamna Ganduje, Farfesa Hafiz, Abdulmuminu da Doguwa

Gwamna Ganduje ya kawo ƙarshen rikici tsakanin Abdulmuminu da Doguwa (Hotuna)

Abdulmuminu da Doguwa

Gwamna Ganduje ya kawo ƙarshen rikici tsakanin Abdulmuminu da Doguwa (Hotuna)

Jigajigan APC tare da Abdulmuminu da Doguwa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Abin tausayi, yan gida duk duk makafi

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel