Buhari na mika sakon gaisuwarsa ga ‘yan Najeriya – Aisha Buhari

Buhari na mika sakon gaisuwarsa ga ‘yan Najeriya – Aisha Buhari

- Uwargidan shugaban kasa Buhari ta yi ma al’umman Najeriya albishir da cewa shugaban kasar na nan yana samun sauki sosai

- Aisha Buhari ta isar wa ‘yan Najeriya da sakon shugaban kasa Buhari na gaisuwa tare da godiya ga jama’ar kasar sa

- Sannan kuma ta ce ya jinjina wa mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo

Uwargidan shugaban Kasar Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta jadaddawa wa ‘yan Najeriya cewa maigidanta kuma shugaban kasa na samun sauki sosai kamar yadda ya kamata.

Aisha ta fadi hakan ne a filin jirgin sama na Abuja a lokacin da ta dawo daga dubiyar lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke kasar Britaniya yana ganin likitocinsa.

KU KARANTA KUMA: Limamin coci ya bukaci Buhari da ya yi murabus idan al’amarin lafiyarsa ya ki cinyewa

Ta kara da cewa Buhari na samun lafiya kuma ya na mika sakon gaisuwarsa da tarin godiyarsa ga al’umman Najeriya bisa addu’oin da suke ta yi masa sannan kuma suke kan yi masa.

Bayan haka kuma ya jinjina wa mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo kan yadda ya ke gudanar da mulkin kasar ba tare da gazawa ba.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com wanda a ciki ne Sarkin Kano Sanusi Lamido ya soki tsarin gwamnatin kasar

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel