Ban yarda cewa wai mutane 25,000 ne suka koma APC a jihar Kebbi ba, duk tatsuniyace kawai – Makarfi

Ban yarda cewa wai mutane 25,000 ne suka koma APC a jihar Kebbi ba, duk tatsuniyace kawai – Makarfi

- Ahmed Makarfi ya musanta zargin yawan mutanen da Jam’iyyar APC tace sun sauya sheka a jihar Kebbi a makon da ya gabata

- Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da wadansu magoya bayan jam’iyyar 25,000 ne aka ce sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC

Shugaban Jam’iyyar PDP, Ahmed Makarfi ya musanta zargin yawan mutanen da Jam’iyyar APC tace sun sauya sheka a jihar Kebbi a makon da ya gabata.

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da wadansu magoya bayan jam’iyyar 25,000 ne aka ce sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Shugaban jam’iyyar Bello Doya ne ya jagoranci masu sauya shekar.

Ban yarda cewa wai mutane 25,000 ne suka koma APC a jihar Kebbi ba, duk tatsuniyace kawai – Makarfi

Ahmed Makarfi ya musanta zargin yawan mutanen da Jam’iyyar APC tace sun sauya sheka a jihar Kebbi a makon da ya gabata

Gwamnan jihar Abubakar Bagudu da wadansu ’yan jam’iyyar daga kananan hukumomi 21 ne suka karbe su a wata kwarya-kwaryar walima da akayi a Birnin Kebbi.

A jawabinsa gwamnan jihar yayi maraba da su sannan yace jam’iyyar APC za ta yi aiki da su kamar kowani dan jam’iyyar ba tare da nuna wariya ko son kai ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari na mika sakon gaisuwarsa ga ‘yan Najeriya – Aisha Buhari

Kakakin masu sauya shekar Isah Argungu ya ce gaba dayansu sun koma jam’iyyar APC ne saboda kyawawan ayyukan da gwamnatin jihar da na kasa ke yi wa mutanen da suka zabe su.

A halin yanzu, Makarfi ya ki amincewa da yawan mutanen da akace wai sun koma jam’iyyar APC din a jihar Kebbi domin ya ce a saninsa fadar dakin taro na fadar gwamnatin jihar Kebbi din zai iya daukan mutane 5000 ne kawai ba 25,000 kamar yadda akace wai sun halarci bukin sauya shekar.

Makarfi dai bai bada adadin yawan mutanen da suka sauya shekar ba ko da ya fadi hakan.

NAIJ.com ta lissafo maku nasarorin shugaba Buhari a shekaru biyu da ya yi kan mulki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel