Garin tsallaka titi, Ɗan Achaɓa yayi ciki da ɗalibin Jami’a

Garin tsallaka titi, Ɗan Achaɓa yayi ciki da ɗalibin Jami’a

- Dan Achaba a garin Abuja ya kade dalibin Jami'ar Abuja

- Dalibin ya rasu yayin da aka garzaya da shi Asbiti

Wani dan Achaba dake tsananin manna gudu ya make wani dalibin ajin farko na jami’ar Abuja mai shekaru 22 a garin Gwagwalada, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Dalibin mai suna Ayatullah Galadima yana karantar ilimin fahimtar mu’amalar mutum ne a jami’ar Abuja, kuma ya gamu da ajalinsa ne da misalin karfe 3 na ranar Talata 6 ga watan Yuni.

KU KARANTA: Sojoji sun yi ram da masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane

Wani dan uwan mamacin mai suna Aliyu ya shaida ma majiyar NAIJ.com cewar lamarin ya faru ne a titin Park a lokacin da mamacin ya fito daga banki, zai tsallaka titi.

Garin tsallaka titi, Ɗan Achaɓa yayi ciki da ɗalibin Jami’a

Ganagncin Yan Achaɓa

“Akwai wani dansanda a wajen da hatsarin ya faru, kuma shine ya garzaya da Galadima Asibitin koyarwa na jami’ar Abuja, inda a nan ne ya riga mu gidna gaskiya.” Inji Aliyu.

Aliyu yace, tuni aka garzaya da gawar Galadima zuwa kauyen Rubochi inda aka yi masa jana’iza kamar yadda musulunci ya tanadar.

Shima shugaban sashin kula da harkokin dalibai na jami’ar, Dakta Petr Adakayi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya ake ciki da lafiyar Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel