Ramadana: Rundunar Yansanda ta hana Tashe a Kano

Ramadana: Rundunar Yansanda ta hana Tashe a Kano

- Matsalar tsaro ta sabauta haramta Tashe a jihar Kano

- Yansanda sun dau alwashin kama duk wanda yayi Tashe a Kano

Rundunar Yansandan jihar Kano ta haramta yin Dadaddiyar al’adar Hausar nan da aka fi yi a watan Azumi wato Tashe, inda tayi gargadin duk wanda aka kama yana, tabbas yayi kuka da kansa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Kwamishinan Yansandan jihar, Rabi’u Yusuf yana sanar da haka a ranar Talata 6 ga watan Yuni, inda yace sun samu rahoton tsaro dake nuna wasu gungun yandaba na shirin kai abokan gabar su hari da sunan tashe.

KU KARANTA: Uwargidar gwamna El-Rufai ta raba ma masu cutar sikila magunguna

“Rahotannin sirri sun tabbatar mana da wasu yandaba na shirin amfani da daman Tashe don su kai farmaki kan abokan gabarsu, wanda zai iya zama mai kan uwa da wabi kan duk wanda suka gamu da shi. Sakamakon hakan, rundunar ta dakatar da yin Tashe a Azumin bana, kuma zamu kama duk wanda ya karya dokar.” Inji shi.

Ramadana: Rundunar Yansanda ta hana Tashe a Kano

Yara, yan Tashe

Majiyar NAIJ.com tace kwamishinan yayi alwashin ba zasu bari wasu jama’a kalilan su tayar da hankulan mutane ba musamman a wannan wata na Ramadana, daga nan ya shawarci iyaye su ja kunnen yayansu daga gabatar da kowanne irin Tashe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kake ganin yiwuwar dawowar Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel