Toh fa: Majalisa zata bincike gwamnatin Buhari

Toh fa: Majalisa zata bincike gwamnatin Buhari

- Majalisar dattijan Najeriya ta ce zata bincike gwamnatin tarayya kan shirin tsabtace yankin Ogoni

- Gwamnati ta kaddamar da shirin tsabtace yankin Ogoni a shekara 2016 inda a ke bukatar kudi dalla Amurka biliyan 1.

- Sanata Magnus Abe ya bukaci gwamnatin tarayya da ta inganta shirin farfadowar muhali wanda zai kula da al'amurran da suka shafi muhali a kasar

Majalisar dattijan Najeriya a ranar Talata, 6 ga watan Yuni ta kaddamar cewa zata bincike gwamnatin shugaba Muhamadu Buhari kan shirin tsabtace yankin Ogoni, majalisar ta umarni kwamitintin kan yanayi da ta gudanar da bincike kan aiwatar da shirin.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin a shekara 2016 inda a ke bukatar kudi dalla Amurka biliyan 1.

NAIJ.com ta ruwaito cewa majalisar ta yanke shawarar ne bayan wani motsin da shugaban kwamitin majalisar dattawa kan muhalli, sanata Oluremi Tinubu ta gabatar a ranar muhalli ta duniya.

Toh fa: Majalisa zata bincike gwamnatin Buhari

Shirin tsabtace yankin Ogoni na gwamnatin shugaba Muhamadu Buhari

Majalisar dattijai ta kuma umarni kwamitin ta tantance irin ci gaban da aka samu a wani shirin ‘Great Green Wall Program’ na gwamnati da aka kaddamar don sarrafa kwararowar hamada a kasar.

KU KARANTA: Majalisan dattawa tayi kira ga NCC ta ci taran kamfanonin sadarwa bisa ga rashin kyawun cibiyar sadarwa

A nasa gudunmawa, sanata Magnus Abe ya bukaci gwamnatin tarayya da ta inganta shirin farfadowar muhali wanda zai kula da al'amurran da suka shafi muhali a kasar.

A cikin jawabinsa na bikin zagayowar ranar damokradiyya ta shekara 2017 mukaddashin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce cewa tsabtace yankin Ogoni shiri ne wanda ke da muhimmanci ga gwamnatin tarayya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Gidan talabijin na NAIJ.com ta tambayi mutane ko ya kamata shugaba Buhari ya mika wa mataimakinsa mulki kamar yadda wasu 'yan Najeriya ke cewa, ku ji ra'ayoyin su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel