Limamin coci ya bukaci Buhari da ya yi murabus idan al’amarin lafiyarsa ya ki cinyewa

Limamin coci ya bukaci Buhari da ya yi murabus idan al’amarin lafiyarsa ya ki cinyewa

- Wani babban limamin coci dake Lagas, Fasto Adewale Martins, y aba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara

- Fasto Martins ya shawarci shugaban kasar da dauki matakan da suka dace don tabbatar da cewa rashin lafiyar sa bai shafi ci gaban kasar ba

- Ya bayyana ra’ayin sa ne a yayinda yake zantawa da manema labarai a Lagas

Babban limamin cocin Lagas, Fasto Adewale Martins ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da cewa rashin lafiyarsa bai shafi ci gaban kasar ba.

Limamin cocin ya yi wannan sharhin ne a lokacin wani taron manema labarai a Lagas domin bikin cikar sa shekaru 58 a duniya.

A cewar sa, zai fi dacewa shugaban kasar ya yi murabus idan rashin lafiyar sa ba zai bari ya yi aiki daidai da yadda mutane ke tsammani ba.

KU KARANTA KUMA: Tsarin TSA na Buhari bai da amfani Inji wani tsohon Gwamnan CBN

Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta girmama umurnin kotu ta saki wadanda ke a tsare har yanzu.

A halin da ake ciki, tsohon minstan dake kula da tashi da saukan jiragen sama na Najeriya, Cif Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa babu bukatar kasar Najeriya ta kasance daya idan har baza’a sake fasalin al’amuran tarayya ba.

Ministan ya mai da martani ne ga wani jawabi da ministan shari’a kuma alkalin alkalai na tarayya, Abubakar Malami ya yi na cewa baza’a iya sake fasalin al;amuran Najeriya ba a yanzu.

Kalli mukaddashin shugabna kasa Yemi Osinbajo na magana game da yakin Biyafara a NAIJ.com TV:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel