Tsarin TSA na Buhari bai da amfani Inji wani tsohon Gwamnan CBN

Tsarin TSA na Buhari bai da amfani Inji wani tsohon Gwamnan CBN

– Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya ya soki Gwamnatin Buhari

– Farfesa Charles Soludo yayi tir da tsarin TSA na bai daya

– Soludo ya kuma soki wasu tsarin tattalin kasar

Farfesa Soludo ya zargi Gwamnatin Buhari da kawo tsare-tsaren da su dace ba.

Soludo dai masani ne a harkar tattalin arziki.

Gwamnatin Buhari ta maida kaf kudin Gwamnatin zuwa akawun guda.

Tsarin TSA na Buhari bai da amfani Inji wani tsohon Gwamnan CBN

Tsohon Gwamnan CBN ya soki Gwamnatin Shugaba Buhari

Farfesa Charles Soludo wanda yayi Gwamnan CBN a lokacin mulkin Obasanjo ya soki Gwamnatin Shugaba Buhari game da tsarin da ta kawo na TSA watau asusun bai daya wanda yace hakan na da matsala.

KU KARANTA: Jonathan ya kashe kasar nan Inji Soludo

Tsarin TSA na Buhari bai da amfani Inji wani tsohon Gwamnan CBN

Soludo ya soki Tsarin TSA na Gwamnatin Shugaba Buhari

Soludo yace wannan zai hana Jama’a su juya kudin Gwamnatin kasar. Farfesan ya kuma soki yadda Gwamnatin ta rika kayyadewa Dala farashi yace sam ba a yin wannan yayin da ake cikin matsin tattali.

Kuna sane da cewa dai tsohon Gwamnan babban bankin Najeriyan yace tsare-tsaren Shugaba Goodluck Jonathan ne su ka kashe tattalin kasar nan. Soludo yace facaka kurum aka yi lokacin Jonathan don haka dole aka shiga matsala.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Shin Dan Sanda abokin kowa ne ko kuwa?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel