Ashe Shugaba Jonathan ne ya dagargaza tattalin arzikin kasar nan

Ashe Shugaba Jonathan ne ya dagargaza tattalin arzikin kasar nan

– Tsohon Gwamnan CBN yace tsarin shugaba Jonathan ya kashe Najeriya

– A cewar Farfesa Charles Soludo, Jonathan ne ya jefa Najeriya cikin matsin tattali

– Farfesa Soludo yayi Gwamnan CBN a lokacin mulkin Obasanjo

Soludo ya zargi Gwamantin Jonathan da jefa Najeriya cikin kangi

A baya dai Soludo ya taba zargin Gwamnatin Buhari da wannan laifi

Yanzu dai karfin tattalin arzikin Najeriya ya ja baya

Farfesa Charles Soludo

Tattalin arziki: Jonathan ya kashe Najeriya-Soludo

Tsohon Gwamnan babban bankin CBN Farfesa Charles Chukwuma Soludo yace tsare-tsaren Shugaba Goodluck Jonathan ne su ka kashe tattalin kasar nan. Soludo yace facaka kurum aka yi lokacin Jonathan don haka dole aka shiga matsala.

KU KARANTA: Kotu ta mikawa Gwamnatin Najeriya kudin Ikoyi

Ashe Shugaba Jonathan ne ya dagargaza tattalin arzikin kasar nan

Tsohon Gwamnan CBN yace Jonathan ya rusa tattalin arziki

Soludo yace Najeriya ta kashe duk kudin da ta samu lokacin man fetur na tsada a Duniya, da abubuwa su ka canza kuma aka shiga cikin halin ni-‘yasu a kasar tun dama ba ayi wani tanadi ba. Soludo ya bayyana haka ne da yake magana a Jami’ar Jihar Anambra.

Kwanaki dai Farfesan yace babu mutane masu tunani a Gwamnatin Buhari. A wancan lokaci Farfesa Soludo ya bayyana yadda Gwamnatin Buhari ta jawo durkushewar tattalin arzikin Najeriya.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Azumi ya canza farashin kaya a kasuwa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel