Ana talauci a Bauchi, amma dubi me gwamnati tayi da kudin talakawa

Ana talauci a Bauchi, amma dubi me gwamnati tayi da kudin talakawa

- Gwamnati ta kashe makudan kudade don kawo dawaki ga kasashen sarautun cikin jihar Bauchi

- Gwamnati tace raya al'adu abu ne muhimmi, kuma sarakunan gargajiyar ne suka bukaci hakan

- Masarautu 6 ne suka amfana da sabbin zubin

Gwamnatin jihar Bauchi ta kashe miliyan dari kan dawakai, duk da talakawa na kukan na tuwo. Bayan kuma sayo dawakin, gwamnati ta kare kudurin nata da cewa raya al'adu na da matukar muhimmanci.

Kwamishinan kananan hukumomin jihar Mal. Nasirudden muhammad ne ya furta hakan inda yace a cikin shekaru biyun da suka gabata, N96m suka kashe kan sayo wa masarautun gargajiya 6 na jihar dawaki don abun da sarakunan suka bukata kenan.

Masarautun sun hada da na Bauchi, Dass, Ningi, Misau, Jama'are da Katagum.

Ana talacin a Bauchi, amma dubi me gwamnati tayi da kudin talakawa

Ana talacin a Bauchi, amma dubi me gwamnati tayi da kudin talakawa

A rahotonta na shekarar 2015 dai, majalisar dinkin duniya, ofishi mai kula da ci gaban kasashe, yace kashi 87 cikin dari na jama'ar jihar talakawa ne na futuk.

KU KARANTA KUMA: Buhari na mika sakon gaisuwarsa ga ‘yan Najeriya – Aisha Buhari

Kwamishinan ya kuma bada wasu alkalumman na kiyasin kudin da gwamnati ta kashe kan biya wa wasu kananan hukumomin jihar basukan da suka kasa biya, buga takardun bai-daya na jiha da ma wasannin jiha don nishadi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Kalli wannan bidiyo na NAIJ.com kan ra'ayin jama'a game da dawowar Buhari nan bada jimawa ba

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel