Majalisan dattawa tayi kira ga NCC ta ci taran kamfanonin sadarwa bisa ga rashin kyawun cibiyar sadarwa

Majalisan dattawa tayi kira ga NCC ta ci taran kamfanonin sadarwa bisa ga rashin kyawun cibiyar sadarwa

Majalisan dattawa a yau Talata tayi ca akan rashin kyawun hanyoyin sadarwa da kamfanonin sadarwa ke baiwa yan Najeriya.

A wata maganar da Sanata Andy Uba ya samar, ya bayyana cewa yawan rashin kyawun sadarwa a Najeriya babban cuta ne inda an ci ma Yan Najeriya biliyoyin kudi.

Yayinda yake bayanin rashin kyawun sabis, Uba yace, “Yan Najeriya basu jin magana idan suna waya tamkar mutum na magana cikin ruwa."

Ya jaddada cewa kamfanonin sadarwa na satan kudaden mutane kawai ba tare biyan bukatan mutanen ba.

Uba yace bai dace a dinga cire kudin mutane ba tare bukatunsu ya biya ba saboda idan mutum bai biya bukatanshi kum aka cire masa kudi zalunci ne.

Majalisan dattawa tayi kira ga NCC ta ci taran kamfanonin sadarwa bisa ga rashin kyawun cibiyar sadarwa

Majalisan dattawa tayi kira ga NCC ta ci taran kamfanonin sadarwa bisa ga rashin kyawun cibiyar sadarwa

Ya kara da cewa kamfanonin sadarwa sun kasance basu bin umurnin hukumar saboda haka, majalisar dattawa ta tilastawa kamfanonin su mayarwa mutane da kudinsu idan bukatunsu bai biya ba.

KU KARANTA: Asirin Dino Melaye ya tonu

Daga cikin maganganun da akayi shine hukumar sadarwan Najeriya da sauran ma’aikatun gwamnati da ke da alaka da hakan su gudanar da bincike kan abinda yasa ake samun matsala kuma a gyara.

https://web.facebook.com/naijcomhausa/?ref=bookmarks#

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel