Uwargidar gwamna El-Rufai ta raba ma masu cutar sikila magunguna

Uwargidar gwamna El-Rufai ta raba ma masu cutar sikila magunguna

- Hadiza Isam El-Rufai ta baiwa masu dauke da cutar Sikila magunguna

- Hadiza ta shawarci yan mata da samari da su tabbata sun gudanar da gwaje gwaje

Uwargidar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Isam El-Rufai ta baiwa masu dauke da cutar Sikila magunguna ta hannun cibiyar tallafa ma masu cutar Sikila.

Yayin mika kayayyakin ga cibiyar, Hadiza ta jaddada bukatar ganin an samar da soyayya ga marasa lafiyan da kulawa duk a garesu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Sojoji sun yi ram da masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane

Hajiya Hadiza ta kara bada shawara ga yan mata da samari da su tabbata sun gudanar da gwaje gwaje domin tantance matsayinsu dangane da cutar Sikila.

Uwargidar gwamna El-Rufai ta raba ma masu cutar sikila magunguna

cutar sikila

A nata jawabin, kwamishinan kula da harkokin mata Hajiya Hafsat Baba ta bayyana cewar a duk duniya ba kasar data kai Najeriya yawan masu sikila, inda tace:

“A duk mutane 4 yan Najeriya, mutum daya na dauke da cutar sikila, ana haihuwar jarirai 150,000 masu dauke da cutar a kasar nan” Inji Hafsat.

Uwargidar gwamna El-Rufai

Uwargidar gwamna El-Rufai

Kwamishinan tace an yi amfani da damar ne domin magance watsuwar cutar sikila, kuma zasu cigaba da bin duk wata hanya data dace don magance cutar da suka hada da gudanar da bincike, bada shawarwari, gwaje gwaje da sauransu.

A nata jawabin, majiyar NAIJ.com ta jiyo shugaban cibiyar, Hajiya Badiya ta yaba ma uwargidar gwamnan sakamakon tallafin data baiwa marasa lafiya, ta bayyana cewar cibiyarsu nada rajistan marasa lafiya 6000 dake karbar magani kyauta a duk wata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kuke ganin dawowar Baba Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel