Shahararren musulmin dan wasa Cheick Tiote ya yanke jiki ya rasu a filin wasa

Shahararren musulmin dan wasa Cheick Tiote ya yanke jiki ya rasu a filin wasa

- Tsohon dan wasan Newcastle na tsakiya Cheick Tiote ya rasu yana da shekara 30 bayan ya fadi a lokacin da yake atisaye da kungiyarsa ta China Beijing Enterprises.

- Mai magana da yawun dan wasan Emanuele Palladino ne ya tabbatar da mutuwar tasa a ranar Litinin din nan.

Cheick Tiote ya yi wa kasarsa Ivory Coast wasa inda suka dauki kofin kasashen Afirka na shekara ta 2015.

A kwanan nan ya koma China da wasa bayan ya dade a gasar Premier tare da Newcastle United.

Shahararren musulmin dan wasa Cheick Tiote ya yanke jiki ya rasu a filin wasa

Shahararren musulmin dan wasa Cheick Tiote ya yanke jiki ya rasu a filin wasa

NAIJ.com ta samu labarin cewa dan wasan na Ivory Cosat ya yi wa Newcastle wasan Premier 139 tun bayan da ya koma can a watan Agusta na 2010 daga FC Twente toa Holland.

Wasa uku kawai dan wasan mai shekara 30 ya yi wa Newcastle din a bana, kafin ya koma kungiyar ta China a kan kudin da ba a bayyana ba.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel