Toh fa: Kotu ta saki wani dan kuna bakin wake bayan shekaru 4 a tsare

Toh fa: Kotu ta saki wani dan kuna bakin wake bayan shekaru 4 a tsare

- Babban kotun tarayya da ke Abuja ta saki Usman Abubakar wanda a ke zargi da ta’addanci

- Ana zargin Abubakar da hannu ga sace wasu 'yan kasashen waje 7 a Bauchi

- An gurfanar da Abubakar tare da wasu mutanen 6 bisa caji 11

Wani babban kotun tarayya da ke Abuja, a yau Talata, 6 ga watan Yuni ta sallami Usman Abubakar wanda a ke zargi dan kungiyar Boko Haram ne, an gurfanar da shi tare da wasu mutane 6 da a ke kuma zargin su da ta’addanci.

Abubakar wanda a ke zargi da hannu ga sace wasu 'yan kasashen waje 7 daga wurin gine-gine a Bauchi, wadanda aka dauka zuwa dajin Sambisa, a Borno, inda kuma aka kashe su a watan Fabrairu ta shekara 2013.

An dora masa laifi tare da Mohammed Usman (wanda aka sani da Khalid Al-Barnawi), Mohammed Bashir Saleh, Umar Mohammed Bello (wanda aka sani da Abu Azzan), Mohammed Salisu (wanda aka sani da Datti), Yakubu Nuhu (wanda aka sani da Bello Maishayi) da kuma wata mace, Halima Haliru.

Toh fa: Kotu ta saki wani dan kuna bakin wake bayan shekaru 4 a tsare

Babban kotun tarayya da ke Abuja

NAIJ.com ta ruwaito cewa an gurfanar da Abubakar tare da mutanen 6 bisa caji 11 a kan sace da kuma kashe ‘yan kasashen wajen.

KU KARANTA: Sojoji sun yi ram da masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane

Alƙali, mai shari’a John Tsoho, a cikin wani gajeren hukuncin, ya saki Usman Abubakar wanda ya shafe shekaru 4 a tsare.

Tsoho ya dakatad da sharia’an sauran mutanen har zuwa ranar 19 da kotu zata ci gaba da sauraran karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon zanga-zangar tunawa da 'yan matan Chibok bayan shekaru 3 da sace su

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yi alkawarin tallafa wa hukumar FRSC

Gwamnatin Kano za ta tallafa wa hukumar FRSC don rage haɗura a hanyoyi
NAIJ.com
Mailfire view pixel