2019: Wadanda zasu iya gadar Buhari in ya bar mulki

2019: Wadanda zasu iya gadar Buhari in ya bar mulki

- Koda Buhari ya sami damar karasa wa'adin mulkinsa zayyi wuya ya sami isasshen goyon baya ya sake takara a jam'iyyarsa ta APC, domin a lokaci yana kusantar shekaru 80 ne da haihuwa

- Ga dukkan alamu shugaba Buhari basshi da isashiyar lafiyar da zai sake tsayawa takara a karo na biyu

- Buhari zai iya zabo wani cikin gwamnoni ko jiga-jigan siyasa a cikin jam'iyyar APC ya gaje shi, idan su Bola Tinubu basu yi masa tawaye ba

A lokacin da ake buga kugen siyasa na shekarar 2019, tuni dai masu sharhin siyasa ke ganin akwai yiwuwar Najeriya zata sake samun sabon shugaba duba da yadda shugaba Buhari ke nuna rashin isashiyar lafiya da gajiyawa saboda tsufa da girman matsalolin da ya taras.

Zamu yi duba ga me ka iya zuwa a watanni 18 masu zuwa wanda a lokacin hukumar Zabe ke shirin gudanar da zabukan gwamnoni da na shugaban kasa, domin tuni ta fitar da jaddawalin yadda take shirin gudanar da zaben wanda a karshen 2018 ko farkon 2019 take so ta kammala shi.

KU KARANTA KUMA: Limamin coci ya bukaci Buhari da ya yi murabus idan al’amarin lafiyarsa ya ki cinyewa

Wadanda zasu iya gadar Buhari in ya bar mulki

2019: Wadanda zasu iya gadar Buhari in ya bar mulki

Idan hasashen ya tabbata, cewa nune ce shugaba Buhari zayyi, anfi ganin ta a haka;

1. Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufai, a dauko gwamnan Imo Rochas Okorocha a matsayin mataimaki, domin farantawa kabilar Ibo masu son ballewa daga Najeriya rai. Shi kuwa Malam zai dauko Malama Hadiza Bala Usman ta hukumar tashar ruwa ne ta taya Mista Bala Bantex mulkar jihar Kaduna.

2. Buhari zai iya zabo Gwamnan Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, a masa auren siyasa da tsohon Gwamna Adams Oshimhole na jihar Edo, domin a dubi koke-koken Arewa maso gabas. Koma a kirawo Hajiya Amina Muhammed ta majalisar dinkin duniya kuma tsohuwar Minista, a samo Oby Ezekwesili tsohuwar ministar ilmi ta taya ta mataimakiya.

3. Idan kuma su Bola Ahmed Tinubu aka bawa zabi, zasu iya dauko tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a hada shi da ko tsohon gwamna mutuminsa Orji Uzo Kalu ko Ken Nnnamani tsohon shugaban majalisar dattijai.

4. Su Bola Tinubu kuma kan iya ma daukar Hon. Yakubu Dogara ko Sam Nda Isaiah ya zama mataimaki ga shi kanshi Bola Tinubu, domin a sirka addinai.

5. Idan kuwa ta rikice tafi karfin jam'iyyar APC aka sami baraka, to tsohon gwamnan Kano Rabi'u Musa Kwankwaso ko Malam Ibrahim Shekarau na iya taka rawa in dattijan kabilun kudancin kasar nan suka mara musu baya.

6. Farfadowar jam'iyyar Adawa ta PDP na iya baiwa Alh. Sule Lamido, ko Goodluck Jonathan ko ma Alh. Namadi Sambo wata damar dawo da tagomashinsu don sake dawowa karagar mulki. Akwai kuma Ali Modu Sheriff tsohon gwamnan Borno, da ma gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose.

7. Idan kuwa ta Allah ce tayi da shugaba Buhari a mulkinsa na farko, to Shugaba Osinbajo na iya takara, ya jawo Malam Nasir El-Rufai ya taya shi, duk da cewa iyaka karashen wa'adin Buhari kawai zai iya yi.

8. Idan kuwa jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyu suka ga baraka, suna iya gamewa su mara wa shugaban majalisar Dattijai Sanata Bukola Saraki baya, su dauko Ken Nnamani ya taya shi a mataimaki.

9. Rawar da tsofin shugabanni irin su Janar Obasanjo, Janar Abdussalami da Janar Babangida zasu taka na iya fito da Col. Sambo Dasuki su mara masa baya ya ci zabe, a hada shi da Donald Duke na Cross Rivers.

10. Ministoci masu karfi suma zasu iya taka rawa a siyasance in suka iya hado kan jam'iyyarsu da jama'ar Najeriya, irinsu Ministan wuta da ayyuka, Babatunde Raji Fashola, da Rotimi Amaechi, suna iya hayewa su bar su Lai Muhammed da kallo.

11. Gwamnonin jam'iyyar APC duk da cewa bassu da farin jini a idon talakawansu, ganin cewa a babbar rigar Buhari suka tsallake, kuma a tafiyar farko suke a siyasance, zasu iya hade kai su jawo Gwamnan Sakkwato su bashi tuta ya ja musu ragama.

12. Shugaba Buhari yana iya murmurewa, ya ajje Osinbajo ya dauko Tinubu ayi tafiya ta biyu dashi don a saka masa wahalarsa ta hado kan yammacin Najeriya.

Wannan dai duk hasashe ne a mahanga irin ta siyasa, siyasar Najeriya na da dambarwa da salo iri-iri inda ba wani aboki ko abokin hamayya, duk dai karshe, wai don talakka ake yi, shi kuwa ya fito rana ya zabi wadanda zasu sake bashi alkawurran da ba lallai su cika masa ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel