'Namadi Sambo ya san da alaka ta da Boko Haram' - Sanata Ndume

'Namadi Sambo ya san da alaka ta da Boko Haram' - Sanata Ndume

- Ana zargin Ndume, kuma ana tuhumarsa da alaka da Boko Haram tun 2011,

- Yana kotu tun 2011 yana kare kansa

- An gano yadda yayi amfani da Boko Haram don razana hukuma

A roko da Sanata Ali Ndume keyi na a rufe karar da ake dashi kan alaka da Boko Haram, Sanata mai wakiltar Borno ta kudu yace duk abinda yayi a lokutan da sanin hukumar DSS da ma kuma mataimakin shugaban kasa na lokacin Namadi Sambo.

An dai kame tare da tuhumar Sanata Ndume tun 2011, bayan sauraron karar da ake yi kansa bisa zaben shekarar, amma sai aka sami 'yan Boko Haram suna razanar da masu shari'ar ta wayar tarho. A karshe dai shari'ar sai Abuja aka dawo da ita.

Kawai garin binciken wayar da ake turo sakonnin ta hanyar sirri, sai aka samu ashe Sanatan ne ke tura yadda mayakan zasu yi masa aikien sakonni ga alkalin.

'Namadi Sambo ya san da alaka ta da Boko Haram' - Sanata Ndume

'Namadi Sambo ya san da alaka ta da Boko Haram' - Sanata Ndume

Daga nan sai aka kwace wayoyinsa aka tuhume shi da alaka da Boko Haram, abun da shi kuma ya musanta. Yace duk abun da yake yi a lokacin yana sanar da Alh. Namadi Sambo da hukumar DSS, kuma ma zargin yana biyan kudi don karfafar ta'addanci kage ne.

Ya dai ce tun kwamitin da shugaban kasa na lokacin ya kafa don samo mafitar sulhu da mayakan ya sami lambar, kuma ta wani saurayi ce a cikin mayakan, wanda tuni aka kame shi aka kuma tabbatar dan Boko Haram ne, kuma yana can ma kulle.

Alkali Kolawale dai bayan sauraron lauya mai kare Ndume, Rickey Tarfa, ya sanya 4 ga watan Yuli don yanke hukunci kan tsohon batun.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara

Yanzu-Yanzu: Dan takarar jam’iyyar APGA Willie Obiano ya lashe zaben gwaman jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel