Sojoji sun yi ram da masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane

Sojoji sun yi ram da masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane

- Dakarun Sojojin Najeriya sun kama masu fasa bututun mai

- Kwamandan rundunar Sojin yankin, Admiral Apochi Suleiman ne ya bayyana haka

Dakarun Sojojin Najeriya sun kama wasu da ake zargin da fasa butayen mai a jihar Bayelsa, ta hanyar amfani da nakiya wajen fasa butayen.

Kwamandan rundunar Sojin yankin, Admiral Apochi Suleiman ne ya bayyana haka a shelkwatar rundunar yayin wata ganawa da manema labaru a babban jihar Bayelsa, Yenagoa. Kwamandan yace:

“Bayan mun samu labarin ayyukan yan fasa bututun mai a yankin ISONOGBENE inda muka kama mutane 3; Ayebemi Dressman, Inimotimi Abule da Epemege Frank.”

KU KARANTA: Watan Ramadana: Naziru ya saki waƙa, ya koma Tafsiri (bidiyo)

Suleiman wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Kanal Danujam Abdullahi ya kara da cewa Sojojin dake jibge a BENESIDE a karamar hukumar Ekeremor sun kama barayin mai su biyu; Bibowa Anemi da Ngoriduwa Gomogo.

Sojoji sun yi ram da masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane

Sojoji

Abdullahi ya kara da cewa Sojojin sun yi artabu da wasu masu garkuwa da mutane, inda suka ceto mutane 2 da aka yi garkuwa dasu, sun kwato makamai Alburusai 23, na’urar bada wuta da kwalekwalen zamani, a yanzu haka mutanen suna samun kulawa a Asibiti a Fatakwal.

Sojoji sun yi ram da masu fasa bututun mai da masu garkuwa da mutane

Masu fasa bututun mai

Daga karshe Abdullahi ya gode ma jama’a da kafafen watsa labaru kan goyon bayan da suke baiwa rundunar Sojin a kokarinta na kare butayen mai da sauran na’urorin mai gaba daya daga miyagun mutane, barayi da yan fashin teku.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ya kake ganin dawowar shugaba Buhari?

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Zaben Anambara yana daga cikin mafi muni zabe da aka gudanar tun 1999 da Najeriya ta dawo mulkin dimokradiyya - Kungiyar PLAC

NAIJ.com
Mailfire view pixel